Sojoji Sun Ceto Mutum 17 Bayan Ragargazan Ƴan Boko Haram a Borno

Sojoji Sun Ceto Mutum 17 Bayan Ragargazan Ƴan Boko Haram a Borno

  • Sojojin Nigeria sun ceto mutane 17 bayan dakile harin yan kungiyar Boko Haram a Borno
  • Onyema Nwachukwu, mai magana da yawun rundunar sojojin Nigeria ne ya sanar da hakan
  • Nwachukwu ya ce lamarin ya faru ne a ranar Laraba 7 ga watan Yuli a Kontori hanyar Maiduguri zuwa Damaturu

Dakarun sojojin Nigeria sun ceto mutane mutane 17 daga hannun yan ta'addan kungiyar Boko Haram, The Cable ta ruwaito.

A cewar sanarwar da direktan watsa labarai na sojojji, Onyema Nwachukwu, an sace mutane 17 yayin harin da aka kai a kan hanyar Kontori zuwa Maiduguri a hanyar Damaturu kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Sojoji Sun Ceto Mutum 17 Bayan Ragargazan Yan Boko Haram a Borno
Dakarun Sojojin Nigeria. Hoto: The Cable
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Ƴan Bindiga Sun Turo Mana Bidiyon Yadda Suka Aurar Da Ƴaƴanmu Mata, Iyayen Ɗaliban Kebbi

Nwachukwu ya ce yan ta'addan da suka zo da yawa, sun kai hari kauyen Auno a jihar amma dakarun sojojin Sector 1 na Operation Hadin Kai suka taka musu birki suka yi musayar wuta.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun kama dilan ESN/IPOB na miyagun kwayoyi, an samu kwayoyin N150m

Sanarwar ta ce:

"Yan ta'addan da suka taho da yawa a ranar Laraba 7 ga watan Yulin 2021 sunyi yunkurin kai hari kauyen Auno ta hanyar titin jirgin kasa da ke kallon garin, amma nan take sojoji suka tare su suka yi musayar wuta mai zafi.
"Bayan dakile harin, dakarun 7 Division Garrison da 212 Battalions sun ceto wasu fararen hula da aka sace su yayin harin da aka kai Kontori hanyar Maiduguri zuwa Damaturu.
"An dauki sunayen wadanda aka ceto din sannan an mika su hannun jami'an yan sandan gaggawa na RRS domin daukan mataki na gaba.

KU KARANTA: An Kama Fasto Da Wasu Mutum Biyu Da Naira Miliyan 15 Na Kuɗaɗen Jabu a Otel

"Idan za a iya tunawa a yayin wannan harin ne sojoji suka yi hatsarin mota yayin amsa kirar neman dauki daga mutanen yankin."

Kakakin sojojin ya ce Faruk Yahaya, babban hafsan sojojin kasa ya jinjinawa dakarun sojojin bisa jajircewarsu wurin kawar da yan ta'addan.

Kara karanta wannan

Hisbah: An kwamushe wasu mutane da ake zargin suna aikata luwadi a jihar Kano

Hotunan Ƴan Boko Haram Da Aka Kama Da Magungunan Ƙarfin Maza Da Wasu Kayayyaki a Borno

A wani labarin, dakarun sojojin Nigeria na Sector 1 Operation Hadin Kai (OPHK) tare da taimakon Yan Sa-Kai na Civilian JTF, a ranar 3 ga watan Yuli sun kama wasu yan ta'addan kungiyar Boko Haram biyu, Premium Times ta ruwaito.

LIB ta ruwaito cewa direktan sashin watsa labarai na rundunar sojoji, Onyema Nwachukwu, cikin sanarwar da ya fitar a ranar Talata ya ce sojojin sun kama wasu kayayyaki da aka siyo domin kaiwa yan ta'addan.

Mr Nwachukwu ya ce sun kama gurneti na hannu, diga daya, mota daya, kekuna biyar, wayoyin salula biyu (Tecno da Infinix), man fetur da man juye.

Ya kuma kara da cewa sojojin sun kwato kwayoyi masu bugarwa da magungunan kara karfin maza, magungunan kwari da sauro, kayan abinci da wasu abubuwan.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Wata jahar Arewa ta dauki Mafarauta 10,000 domin su zama kari ga hukumomin tsaro

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel