Biloniya kike aure: An yi cece-kuce yayin da Zahra Buhari ta ce aure na nufin soyayya mara iyaka a gare ta

Biloniya kike aure: An yi cece-kuce yayin da Zahra Buhari ta ce aure na nufin soyayya mara iyaka a gare ta

  • Diyar shugaban kasa Muhammadu Buhari, Zahra, ta bayyana ra’ayinta game da abun da ta dauki aure a wani sako da ta wallafa a kafar sadarwar zamani
  • Matashiyar ta bayyana yadda aure yake nufin soyayya mara iyaka ta kowane siga, amana, haƙuri da sauransu
  • Sai dai kuma, masu amfani da yanar gizo sun yi martani game da ra'ayin Zahra kan aure yayin da wasu daga cikinsu suka kalubalanci ra'ayinta

Daya daga cikin ‘ya’yan Shugaban kasa Muhammadu Buhari, Zahra, a kwanan nan ta sanya mutane a shafukan sada zumunta tattaunawa bayan ta yi wani wallafa inda ta bayyana abin da aure yake nufi a gare ta.

Zahra ta wallafa wani bidiyo inda ta tara mutane da dama don bayyana ra'ayinsu game da aure. Yayin da wasu daga cikinsu suka bayyana shi a matsayin mai ban sha’awa, wasu kuma sun ce aure na nufin yarda da sauransu.

KU KARANTA KUMA: 2023: Tsohon dan takarar shugaban kasa ya bayyana yadda magajin Buhari zai Fito

Biloniya kike aure: An yi cece-kuce yayin da Zahra Buhari ta ce aure na nufin soyayya mara sharadi a gare ta
Zahra Buhari ta ce aure na nufin soyayya mara sharadi ta kowani siga Hoto: @mrs_zmbi
Asali: Instagram

A rubutun da ke kasan wallafar, matashiyar ta bayyana nata ra'ayin kan lamarin. A cewar Zahra, aure a gareta yana nufin soyayya mara iyaka ta kowane siga.

Bata tsaya nan ba, ta kuma bayyana aure a matsayin hakuri, amana, abota da kwanciyar hankali.

A kalamanta:

“Meye ma'anar aure a gare ku!
“A wurina aure na nufin soyayya ce mara iyaka a cikin salo iri-iri.
“Hakuri, Amana, abota, kwanciyar hankali.”

Kalli wallafarta a kasa:

KU KARANTA KUMA: Buhari ya sassauta, ya amince zai tattauna da 'yan kudu maso gabas kan rabewa

Martani daga mabiya:

Ba da jimawa ba wallafar ya yadu a shafukan sada zumunta kuma hakan ya sa 'yan Najeriya bayyana ra'ayinsu game da batun. Wasu daga cikinsu suna ganin cewa bai kamata Zahra ta yi magana a kan soyayyar mara iyaka ba saboda tana auren mai kuɗi sosai.

Karanta abun da wasun su suka ce a kasa:

Markehis:

"Babu wani abu kamar so mara iyaka sai daga uwa zuwa ga ɗa."

Adaikwerre:

“Wanda ya ci ya koshi ne yake fadawa soyayya balle a kai ga aure, hajiya mahaifinki na bada mana yaji a idanu muyi magana a kan wannan.”

Yusuf_writes:

"Kin auri biloniya kuma kina magana ne akan soyayya mara iyaka."

V.i.c_toriah:

“aure yaudara ne dan Allah.”

Officialginabenson:

"Yana da ma'ana amma menene ma'anar Najeriya ga mahaifinka."

Yusuf Buhari zai auri 'yar Sarkin Bichi, Nasir Ado Bayero

A wani labarin, Yusuf Buhari, dan gidan shugaban kasa Muhammadu, na shirin angwancewa da diyar Sarkin Bichi, Alhaji Nasir Ado Bayero, Zahra Ado Bayero, rahoton Daily Nigerian.

Zahra Bayero yanzu haka na karatun ilmin zanen gine-gine a kasar Birtaniya yayinda shi Yusuf Buhari ya kammala karatunsa a jami'ar Surrey, Guildford, a Birtaniya.

Majiyoyi sun bayyana cewa za'a gudanar da bikin cikin watanni biyu zuwa uku.

Asali: Legit.ng

Online view pixel