Hotunan Yadda Gwamna Ya Cafke Ƴan Daba Suna Yi Wa Masu Motocci Fashi a Kan Titin Legas

Hotunan Yadda Gwamna Ya Cafke Ƴan Daba Suna Yi Wa Masu Motocci Fashi a Kan Titin Legas

  • Babajide Sanwo-Olu, gwamnan jihar Legas da tawagarsa sun cece wani mutum daga 'yan fashin titi
  • Gwamnan da tawagarsa suna wucewa ta unguwar ne sai suka ga wasu mutane uku da adda suna kokarin yi wa mutumin fashi
  • Nan take jami'an tsaro da ke tare da gwamnan suka kama mutanen suka kwace addunan da ke hannuwansu

Gwamnan jihar Legas Babajide Sanwo-Olu a jihar Legas a ranar Litinin ya ceto matafiya daga gungun wasu mutane da suka kware wurin yi wa masu ababen hawa da motocci barazana a kan titi, Daily Trust ta ruwaito.

The Punch ta ruwaito cewa Gbenga Akosile, sakataren watsa labarai na gwamnan Legas ne ya sanar da hakan.

Hotunan Yadda Gwamna Ya Ceci Wani Mutum Daga ‘Ƴan Fashi’ a Kan Titin Legas
Hotunan Yadda Gwamna Ya Ceci Wani Mutum Daga ‘Ƴan Fashi’ a Kan Titin Legas. Credit: The Lagos State Government
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Hotunan Ƴan Boko Haram Da Aka Kama Da Magungunan Ƙarfin Maza Da Wasu Kayayyaki a Borno

Gungun mutanen sun fada hannun hukuma ne a yayin da suka yi yunkurin cin zalin wani mutum matukin mota a kusa da Ojota da Alausa a ranar Litinin.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun gano rashin tasirin hada lamabobin SIM da NIN, ‘yan sanda ba sa iya bin sawun 'yan bindiga

Tawagar gwamnan tana wucewa ta yankin ne a lokacin da wasu maza uku dauke da adduna ke yawo kan titi suna neman wadanda za su zalunta.

Jami'an tsaron da ke tawagar gwamnan, nan take suka cafke wadanda ake zargin, suka kwace addunan da ke hannunsu suka kama su.

Sanwo-Olu ya bayyana kamen a matsayin gargadi ga sauran bata gari da masu niyyar yi wa matafiya fashi a kan hanya cewa bata gari ba su da mafaka a jihar Legas.

Ga hotunan a kasa:

Hotunan Yadda Gwamna Ya Cafke Ƴan Daba Suna Yi Wa Masu Motocci Fashi a Kan Titin Legas
Gwamnan Legas Babajide Sanwo-Olu da tawagarsa sun cafke yan daba a titi. Hoto: The Cable
Asali: Facebook

Hotunan Yadda Gwamna Ya Cafke Ƴan Daba Suna Yi Wa Masu Motocci Fashi a Kan Titin Legas
Yan daba dauke da adduna a titi Legas suna kokarin yiwa masu motocci fashi. The Cable
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: An Kama Fasto Da Wasu Mutum Biyu Da Naira Miliyan 15 Na Kuɗaɗen Jabu a Otel

Hotunan Yadda Gwamna Ya Cafke Ƴan Daba Suna Yi Wa Masu Motocci Fashi a Kan Titin Legas
Jami'an tsaro da ke tare da gwamnan Legas yayin da suka cafle yan daba da ke yi wa mutae fashi a titi. The Cable
Asali: Facebook

Hotunan Yadda Gwamna Ya Cafke Ƴan Daba Suna Yi Wa Masu Motocci Fashi a Kan Titin Legas
Yan daba da tawagar gwamnan jihar Legas ta kama suna kokarin yi wa masu motocci fashi. Hoto: The Cable
Asali: Facebook

Yan fashin titi da ke adabar masu ababen hawa a Legas

Duk da kokarin da gwamnatin jihar Legas ke yi na kawar da bata gari a jihar, mutane sun dade suna kokawa kan yan daba da ke adabar masu ababen hawa.

Kara karanta wannan

Hisbah: An kwamushe wasu mutane da ake zargin suna aikata luwadi a jihar Kano

Ana yawan ganin yadda ake yi wa mutane fashi da tsakar rana a babban titin Legas zuwa Ibadan, Redeem road da Ibafo har zuwa Ojota.

Mutane sun dade suna korafi kan lamarin, wanda hakan daga bisani ya tilasta gwamnatin jihar ta tsaurara matakan tsaro a yankunan.

Hotunan mataimakin kwamishinan Ƴan Sanda na bogi da aka kama cikin otel a Kano

A wani labarin daban, rundunar ƴan sanda na jihar Kano ta kama mataimakin kwamishinan ƴan sanda na bogi a wani otel a birnin Kano, The Punch ta ruwaito.

LIB ta ruwaito cewa mai magana da yawun yan sandan jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna ne ya sanarwa manema labarai hakan a ranar Alhamis.

Haruna ya ce an kama wanda ake zargin, wani Mohammed Aliyu mazaunin Mariri Hotoro Quarters bayan ya gabatar da kansa a matsayin ACP a wani otel a Kano ya kuma nemi a bashi ɗaki ya sauki baƙinsa da ke zuwa daga Kaduna.

Kara karanta wannan

Gwamnan Gombe ya bayyana matakansa da ya dauka na kare dalibai daga sata a makarantu

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: