Wani Babban Mai Faɗa a Ji a Jam'iyyar APC Ya Sauya Sheƙa Zuwa PDP
- Wani babban jigon APC a jihar Gombe ya bayyana ficewarsa daga jam'iyyar zuwa PDP
- Muhammad Barde, wanda tsohon ɗan takarar gwamna ne a Gombe, yace APC ba ta iya shugabanci ba
- Yace tun sanda tsohuwar jam'iyyarsa tace suje su canza rijista, ya fice daga jam'iyyar
Tsohon ɗan takarar gwamna a jihar Gombe kuma babban mai faɗa a ji a jam'iyyar APC ta jihar, Muhammad Barde, ya sauya sheƙa zuwa PDP ranar Litinin, kamar yadda Punch ta ruwaito.
KARANTA ANAN: Da Ɗuminsa: Wasu Yan Bindiga Sun Sake Kai Hari Kaduna, Sun Hallaka Aƙalla Mutum 9
Barde ya shaida wa manema labarai a sakateriyar jam'iyyar PDP a Gombe cewa bai sabunta rijistarsa da jam'iyyar APC ba.
Vanguard ta ruwaito cewa, Barde ya yi rijista da jam'iyyar PDP tun 2 ga watan Fabrairun da ya gabata.
Yace: "Nazo in nuna biyayya ta ne ga jam'iyyar mu ta PDP, domin na fice daga APC tun sanda aka umarce mu da mu sabunta rijistar zama ɗan jam'iyya. Maimakon haka sai naje na yi rijista da PDP."
Babu kyakkyawan shugabanci a APC
Muhammad Barde ya bayyana babban dalilinsa na ficewa daga APC cewa babu kyakkyawan tsarin shugabanci a tsohuwar jam'iyyar tasa.
KARANTA ANAN: Bayan Muƙabala, Rundunar Yan Sanda Ta Gayyaci Sheikh AbdulJabbar Kabara, Ta Faɗi Dalili
A cewarsa: "Ba komai yasa na fice daga APC ba illa rashin jagoranci mai kyau, abinda idunun mu suka shaida mana shine gwamnati ce ta mutum ɗaya, da mutun ɗaya ke tafiyar da ita, kuma zuwa ga mutum ɗaya."
A wani labarin kuma Shehu Sani Ya Caccaki FG Kan Kama Su Nnamdi Kanu, Ya Faɗi Abinda Yafi Muhummanci
Tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, ya bayyana cewa abune mai muhimmanci ga gwamnati da hukumomin tsaro su damƙe shugabannin yan bindiga dake sace mutane a Najeriya.
Tsohon Sanatan yace da gwamnati zata maida hankali kan shugabannin yan bindiga da komai ya dai-daita.
Asali: Legit.ng