Cikakken Bayani: Dalilin da Yasa Shugaban Izala na Kano Ya Kai Ƙarar Sheikh Abduljabbar Kabara
- Rundunar yan sanda a Kano ta gayyaci Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ya bayyana a gabanta ranar Litinin
- Wannan na zuwa kwana biyu kacal da malamin yayi muƙabala da wasu malaman jihar Kano
- Sai dai rundunar yan sanda tace sam gayyatar da ta wa Abduljabbar bata da alaƙa da muƙabalar da ta gudana
Rundunar yan samda ta jihar Kano ta aike wa Sheikh Abduljabbar Kabara, gayyata ya kawo kanshi gare ta domin amsa wasu tambayoyi a ranar Litinin 12 ga watan Yuli, 2021, kamar yadda BBC hausa ta ruwaito.
KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Shehu Sani Ya Caccaki FG Kan Kama Su Nnamdi Kanu, Ya Faɗi Abinda Yafi Muhummanci
Wannan na zuwa ne awanni 48 bayan malamin ya yi muƙabala tsakaninsa da wasu malaman Kano kan wasu maganganu da yake yi a karatunsa.
Kakakin rundunar na jihar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana cewa sam gayyatar da suka wa malamin ba ta da alaƙa da muƙabalar da aka gudanar.
DSP Kiyawa, yace: "Wannan gayyata ba ta da alaƙa da wannan zama da aka yi, dama tun kafin a yi wannan zama akwai waɗanda suka shigar da ƙorafe-ƙorafe a kansa, kuma mun fara bincikawa."
"Dama mun sanya yau a matsayin ranar da za'a dawo domin cigaba da binciken."
Kakakin yan sandan ya bayyana cewa har yanzun ana cigaba da binciken malamin game da ƙarar da aka shigar a kansa.
Waye yakai ƙarar sheikh Abdujabbar kuma laifin me yayi?
Rahotanni sun tabbatar da cewa shugaban ƙungiyar izala reshen jihar Kano, Sheikh Abdullahi Pakistan, shine ya garzaya wurin yan sanda ya shigar da ƙarar malamin.
Pakistan ya shaidawa yan sanda cewa Malam Abduljabbar yana barazana ga rayuwarsa, kuma an shigar da wannan ƙara tun watan Fabrairu.
"Wani saƙo na ji yana yawo a shafukan sada zumunta inda yake cewa a kashe ni, kuma har wasu muƙarabansa na tuntuɓa sun kuma tabbatar min da hakan cewa a gabansu ma ya yi batun," inji Sheikh Pakistan.
KARANTA ANAN: Jega Ya Buƙaci Sanatoci Kada Su Amince da Buƙatar Shugaba Buhari Ta Naɗin Onochie
Tun bayan wannan ƙara, Sheikh Abduljabbar yana kai kansa ofishin rundunar yan sanda lokaci zuwa lokaci amma a wannan karon sai zuwansa ya faɗa ranar Jumu'a ana Gobe muƙabala.
Hakan yasa shehin malamin ya nemi yan sanda su ɗaga masa kafa zuwa ranar Litinin 12 ga watan Yuli.
A halin yanzun Malam Abduljabbar yana jiran hukunci biyu, na farko daga gwamnatin Kano bayan kammala muƙabala ranar Asabar.
A ɗaya ɓangaren kuma zai jira sakamakon binciken da yan sanda suke a kansa na zargin barazana ga Sheikh Pakistan.
A wani labarin kuma Anga Wata a Najeriya, Sarkin Musulmi Ya Faɗi Ranar da Musulmai Zasu Yi Eld-Eil Kabir 1442AH
Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III, ya bayyana ranar Lahadi 11 ga watan Yuli 2021 a matsayin ranar farko a watan Dhul-Hijja.
Sarkin ya bayyana haka ne biyo bayan samun rahotannin ganin wata a wasu sassan Najeriya da ka yi ranar Asabar.
Asali: Legit.ng