Cikakken Bayani: Sanata Shehu Sani Ya Fice Daga Jam'iyyar PRP

Cikakken Bayani: Sanata Shehu Sani Ya Fice Daga Jam'iyyar PRP

  • Tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani, ya fice daga jam'iyyar PRP da yayi takara a 2019
  • Sani ya bayyana haka ne a wata wasiƙa da ya sanya wa hannu ɗauke da adireshin tsohuwar jam'iyyar tasa PRP
  • Jam'iyyar PRP tsohuwa ce domin an ƙirƙire ta tun a jamhuriya ta biyu, kuma Malam Aminu Kano ne ya jagorance ta

Sanata Shehu Sani, wanda ya wakilci mazaɓar Kaduna ta tsakiya a majalisar dattijai ta takwas, ya fice daga jam'iyyar People’s Redemption Party, PRP, kamar yadda Punch ta ruwato.

KARANTA ANAN: Wani Babban Mai Faɗa a Ji a Jam'iyyar APC Ya Sauya Sheƙa Zuwa PDP

Wannan na ƙunshe ne a wata wasiƙa da tsohon sanatan ya sanya wa hannu kuma ɗauke da adireshin jam'iyyar PRP a ranar 9 ga watan Yuli, 2021.

An yiwa wasiƙar take da "Sanarwa a hukumance kan matakin da na ɗauka na ficewa daga jam'iyya."

Kara karanta wannan

Da Ɗuminsa: Malami Ya Gana da Ƙungiyar Inyamurai Ohanaeze Kan Cafke Nnamdi Kanu

Sanata Shehu Sani
Da Ɗumi-Ɗuminsa: Sanata Shehu Sani Ya Fice Daga Jam'iyyar PRP Hoto: independent.ng
Asali: UGC

Wani sashin wasiƙar yace: "Ina farin cikin sanar da ku cewa na ɗauki matakin matsawa daga jam'iyya, kuma wannan matakin zai fara aiki daga yau."

"Ina fatan zamu cigaba da haɗuwa nan gaba a wurin gwagwarmaya, ina muku fatan alkairi."

A cikin wasiƙar tasa, Sani bai faɗi dalilin ficewarsa daga jam'iyyar PRP ba, hakanan kuma bai faɗi jam'iyyar da zai koma ba, kamar yadda channels tv ta ruwaito.

Shehu Sani ya shiga jam'iyyar PRP ne a watan Oktoba 2018, bayan ya fice daga jam'iyyar APC.

An ƙirƙiri jam'iyyar PRP ne tun a jamhuriya ta biyu kuma tsohon sanannen ɗan siyasa, Mallam Aminu Kano, shine ya jagorance ta bayan an sallame shi daga jam'iyyar NPN.

KARANTA ANAN: Da Ɗuminsa: Wasu Yan Bindiga Sun Sake Kai Hari Kaduna, Sun Hallaka Aƙalla Mutum 9

A wani labarin kuma Cikakken Bayani: Yan Bindiga Sun Sako Sarkin Kajuru, Sun Cigaba da Rike Iyalansa

Kara karanta wannan

Cikakken Bayani: Yan Bindiga Sun Sako Sarkin Kajuru, Sun Cigaba da Rike Iyalansa

Alhaji Alhassan Adamu, Sarkin Kajuru a jihar Kaduna, ya kuɓuta daga hannun masu garkuwa da mutane, waɗanda suka sace shi tare da iyalansa.

Sai dai har yanzun sauran mutum 13 da aka sace su tare ciki harda ɗiyarsa suna hannun maharan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel