Da Ɗumi-Ɗumi: Shehu Sani Ya Caccaki FG Kan Kama Su Nnamdi Kanu, Ya Faɗi Abinda Yafi Muhummanci
- Sanata Shehu Sani ya koka kan gazawar gwamnatin tarayya wajen kuɓutar da ɗaliban da aka sace
- Tsohon Sanatan yace da gwamnati zata maida hankali kan shugabannin yan bindiga da komai ya dai-daita
- Yace kama shugabannin taware yana da kyau, amma ba sune kaɗai matsalar Najeriya ba
Tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani, ya bayyana cewa abune mai muhimmanci ga gwamnati da hukumomin tsaro su damƙe shugabannin yan bindiga dake sace mutane a Najeriya, kamar yadda ripples ta ruwaito.
KARANTA ANAN: Jega Ya Buƙaci Sanatoci Kada Su Amince da Buƙatar Shugaba Buhari Ta Naɗin Onochie
Sani, wanda ya zanta da gidan talabishin na Arise tv ranar Litinin, ya koka kan gazawar gwamnatin shugaba Buhari wajen kuɓutar da ɗaliban dake hannun yan ta'adda, musamman a jihar Kaduna.
Tsohon sanatan ya ƙara da cewa kama shugabannin ƙungiyoyin yan bindiga yafi muhimmanci kan kama yan taware da gwamnati ta maida hankali a kai, kamar yadda the cable ta ruwaito.
A cewar Sani: "Mun san shugaban yan bindiga, Dogo Gidi a yankin jihar Zamfara, da kuma Palleri a yanki jihohin Kaduna da Neja."
"Palleri yana yawan turo saƙon murya, inda yake ikirarain yana da ƙarfin sace duk wanda yaga dama. Shi ya jagoranci sace ɗaliban jami'ar Greenfield, kuma yace zai cigaba da sace wasu."
"Kama waɗannan shugabannin ƙungiyoyin yan bindiga guda biyu zai rage yawaitar sace mutane sosai."
Ya yi magana kan kama Nnamdi Kanu da Igboho
Da yake martani kan cafke shugabannin ƙungiyoyin taware, Sani yace:
"Zan iya cewa suna da alaƙa, kuma yana da muhimmanci kama yan taware. Ba wai ina goyon bayan ƙungiyoyin yan taware bane amma nayi imani cewa zasu iya aiki tuƙuru wajen tabbatar da Najeriya ɗaya."
"Waɗannan yan bindiga suna zuwa ne a ɗaruruwansu, ina ganin akwai matsala a cikin jami'an tsaron mu, domin yan taware ba sune kaɗai matsalar Najeriya ba."
KARANTA ANAN: Karin Bayani: An Tabbatar da Ɓullar Sabuwar Cutar COVID19 Mai Kisa a Jihar Oyo
Sanata Shehu Sani ya ƙara da cewa da gwamnati zata maida hankali kan yan bindiga kamar yadda ta yiwa ƙungiyoyin taware da abubuwa sun dai-daita.
A wani labarin kuma Anga Wata a Najeriya, Sarkin Musulmi Ya Faɗi Ranar da Musulmai Zasu Yi Eld-Eil Kabir 1442AH
Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'ad Abubakar III, ya bayyana ranar Lahadi 11 ga watan Yuli 2021 a matsayin ranar farko a watan Dhul-Hijja.
Sarkin ya bayyana haka ne biyo bayan samun rahotannin ganin wata a wasu sassan Najeriya da ka yi ranar Asabar.
Asali: Legit.ng