Cikakken Bayani: Yan Bindiga Sun Sako Sarkin Kajuru, Sun Cigaba da Rike Iyalansa
- Yan bindigan da suka sace Sarkin Kajuru, Alhaji Alhassan Adamu, Sun sako shi da yammacin Litinin
- Sai dai har yanzun sauran mutum 13 da aka sace su tare ciki harda ɗiyarsa suna hannun maharan
- Sarkin yayi ƙoƙarin yin jawabi a gaban jama'a amma sai hawaye suka zubo daga idanunsa
Alhaji Alhassan Adamu, Sarkin Kajuru a jihar Kaduna, ya kuɓuta daga hannun masu garkuwa da mutane, waɗanda suka sace shi tare da iyalansa.
KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗuminsa: Sanata Shehu Sani Ya Fice Daga Jam'iyyar PRP
Wata majiya ta tabbatar da haka ga jaridar dailytrust, ta bayyana cewa ragowar mutum 13 da aka sace su tare a gidansa har yanzun suna hannun ɓarayin.
"Sarkin Kajuru, Alhassan Adamu, ya kuɓuta daga hannun yan bindiga, an sako basaraken daga dazukan dake yankin Kajuru," inji majiyar.
Ɗaya daga cikin iyalan gidan sarkin ya bayyana cewa yana cikin ƙoshin lafiya, amma duk da haka za'a kai shi asibiti domin tabbatar wa, kamar yadda punch ta ruwaito.
Ibrahim Inuwa Ƙajuru, tsohon shugaban ƙungiyar yan jarida NUJ, reshen Kaduna, ya tabbatar da dawowar basaraken.
Ɗan jaridar, wanda mazaunin garin Kajuru ne, yace sarkin ya yi jawabi a fadarsa.
Sai dai har yanzun babu wani cikakken bayani game da an biya ɓarayin kuɗin fansa, amma da farko sun nemi a ba su zunzurutun kuɗi miliyan N200m kafin su saki basaraken.
KARANTA ANAN: Da Ɗuminsa: Wasu Yan Bindiga Sun Sake Kai Hari Kaduna, Sun Hallaka Aƙalla Mutum 9
Sarki ya zubda hawaye yayin da ya haɗu da iyalansa
Sarkin Kajuru, Alhassan Adamu, ya zubda hawaye jim kaɗan bayan isarsa yankin da yake jagoranta.
Yayin da yake ƙoƙarin jawabi ga dandazon mutanen da suka fito murnar dawowarsa amma sai tausayi ya kama shi.
Ya fara cewa: "Mutanen Kajuru...." Amma sai hawaye da tausayi ya kama shi ya kasa ƙarisa maganar da yake son yi.
Basaraken ya rufe fuskarsa na tsawon dakika 21 domin ya iya riƙe yanayin tausayi da yake ciki.
Ɓarayin da suka yi garkuwa da shi sun sake shi da yammacin Litinin bayan sun sace shi da safiyar Lahadin da ta gabata.
A wani labarin kuma Cikakken Bayani: Dalilin da Yasa Shugaban Izala na Kano Ya Kai Ƙarar Sheikh Abduljabbar Kabara
Rundunar yan sanda a Kano ta gayyaci Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara ya bayyana a gabanta ranar Litinin
Wannan na zuwa kwana biyu kacal da malamin yayi muƙabala da wasu malaman jihar Kano
Asali: Legit.ng