Hotuna da bidiyon Ahmed Musa tare da dalleliyar sabuwar amaryarsa sun bayyana

Hotuna da bidiyon Ahmed Musa tare da dalleliyar sabuwar amaryarsa sun bayyana

  • Wasu kyawawan hotunan fitaccen dan kwallon kafa Ahmed Musa tare da wata zukekiyar budurwa sun bayyana
  • Kamar yadda shafin @northern_hibiscus ya wallafa, ya ce zukekiyar budurwar ita ce sabuwar amaryar Ahmed Musa
  • Wannan wallafar kuwa ta janyo cece-kuce da maganganu daban-daban daga jama'a

A daren ranar Lahadi ne hotunan wata zukekiyar budurwa tare da fitaccen dan kwallon kafa Ahmed Musa suka bayyana a shafuka daban-daban na Instagram.

Kamar yadda shafin northern_hibiscus ya wallafa a daren Lahadin, shafin ya saka kyawawan hoton Ahmed Musa tare da wata doguwa farar budurwa mai kyau.

A wallafar ta ce: "Ga amaryar @ahmedmusa718. Kai, ina da abubuwa da yawa da nake son cewa, amma Ahmed Musa mutumina ne. Allah ya sanya alheri. Amarya kam sai da ka zaba ka dirje."

KU KARANTA: An bankado: Duk da tace ta bar siyasa, Onochie ta yi wa APC wallafa a 2020

Hotunan Ahmed Musa tare da dalleliyar sabuwar amaryarsa sun bayyana
Hotunan Ahmed Musa tare da dalleliyar sabuwar amaryarsa sun bayyana. Hoto daga @northern_hibiscus
Asali: Instagram

Ko da Legit.ng ta duba shafin fitaccen dan kwallon kafan, bata ga hotunan ba ko wata alama dake nuna cewa wannan ikirarin gaskiya ne. Sai dai za ta cigaba da kokarin kawo muku karin bayani nan gaba kadan.

Kara karanta wannan

Yadda 'yan gudun hijira suka haifi jarirai sama da 17,000 a sansaninsu na jihar Borno

Ga hotunan kamar yadda suke a wallafar.

KU KARANTA: Tsoho mai shekaru 90 ya shiga hannun NDLEA kan safarar miyagun kwayoyi

A wani labari na daban, mukabalar da aka dade ana jira tsakanin Sheikh Abduljabbar da sauran malaman Kano ta kare da rigima domin an kasa tsayawa a tsayayyar matsaya.

Bayan kammala mukabalar, Daily Trust ta gano cewa an shirya mika malamin gaban kotu kan laifukan batanci. 'Yan sanda sun mika takarda domin ya bayyana a gaban hedkwatar 'yan sanda a ranar Litinin.

Wata majiya makusanciya da malamin ta sanar da Daily Trust cewa tuni dama an shirya wadannan zargin kan Abduljabbar wanda aka shirya dauka daga wurin mukabalar wacce aka yi a hukumar Shari'a ta jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Online view pixel