'Yan Sanda da Jami’an DSS Sun Yi Wa Cocin Dunamis Ƙawanya a Abuja

'Yan Sanda da Jami’an DSS Sun Yi Wa Cocin Dunamis Ƙawanya a Abuja

  • Jami'an tsaro da suka kunshi yan sanda da jami'an DSS sun mamaye unguwar da cocin Dunamis ya ke a Abuja
  • 'Yan sandan da sauran jami'an tsaron sun isa wurin ne domin kare yiwuwar kutse daga mambobin masu zanga-zangar #Revolutionnow
  • A ranar Lahadi da ta gabata, jami'an DSS sun kama mutum biyar 'yan #Revolutionnow sanye da riga mai rubutun 'Buhari Must Go' a cocin

Ana zaman dar-dar a cocin Dunamis da ke Lugbe Abuja bayan yan sanda da wasu jami'an tsaro masu farin kaya sun zagaye yankin da cocin ya ke saboda tsoron yiwuwar kutsen mambobin #Revolutionnow da ke zanga-zangar kama wasu mambobinsu da DSS suka yi, The Guardian ta ruwaito.

A yayin da The Guardian ta ziyarci cocin a safiyar ranar Lahadi, ta gano yan sanda da dama a yankin, yayin da motoccin sintiri kimanin guda hudu sun tsaya a wasu muhimman wurare a unguwar.

Kara karanta wannan

Gowon: Ku koma ga Allah, rashin tsaro zai kare a Najeriya nan kusa, ya bayyana mafita

DUBA WANNAN: Ka Yafe Wa Igbobo, Ya Wahala, Ya Gane Kurensa: Basaraken Yarbawa Ya Roƙi Buhari

'Yan Sanda da Jami’an DSS Sun Yi Wa Cocin Dunamis Ƙawanya a Abuja
Jami'an hukumar DSS. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Mai rajjin kare hakkin bil-adama da goyon bayan demokradiyya, Omoyele Sowore, ya yi barazanar sake yin wata gagaruman zanga-zanga idan ba a sako mutane biyar da aka kama sanye da riga mai rubutun 'Buhari Must Go' ba a ranar Lahadi da ta gabata a cocin.

Wadanda aka kama kuma aka tsare a hannun yan sandan farin kaya DSS sune Emmanuel Larry, Henry Nwodo, Samuel Gabriel, Ben Manasseh da Anene Udoka.

KU KARANTA: Sarki mai daraja ta ɗaya a Arewa ya rasu bayan shekaru 45 kan karagar mulki

Sowore, yayin wata taron manema labarai da ya kira a Abuja, a karshen mako, da wata kungiya mai sunan 'Take it Back Movement' ta shirya ya kuma yi ikirarin cewa shugaban kuma babban fasto a cocin Dunamis, Fasto Paul Enenche, ya hada baki da DSS ne domin a kama mutanen.

Kara karanta wannan

Da duminsa: 'Yan bindiga sun yi awon gaba da Sarkin Kajuru tare da iyalansa 13

Matasan Tibi Sun Yabawa Buhari Kan ‘Ragargazan’ Nnamdi Kanu da Sunday Igboho

A wani rahoton, kungiyar matasan Tibi, TYC, ta marawa Shugaba Muhammadu Buhari baya game da matakan da ya dauka kan masu yunkurin ballewa daga kasa, musamman sake kama shugaban haramtaciyyar kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu da samamen da DSS ta kai gidan Sunday Igboho, Leadership ta ruwaito.

Kungiyar cikin sanarwar da ta fitar mai dauke da sa hannun shugabanta, Mike Msuaan, ta ce rashin daukan kwararan matakai a kan masu yunkurin ballewa daga Nigeria zai kara dilmiya kasar cikin matsaloli ne fiye da yadda ake zato.

Leadership ta ruwaito cewa Mr Msuaan ya jinjinawa kokarin gwamnatin tarayya, musamman ta hanyar amfani da hanyar diflomasiyya don sake kama Kanu, hakan ya jadadawa yan Nigeria cewa shugaban kasa ba zuba wa bata gari da masu son ballewa daga kasa ido ya ke yi ba.

Kara karanta wannan

Sabon hari: 'Yan bindiga sun yi awon gaba da wasu yara bayan raba su da mahaifiyarsu a Kaduna

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164