Wani Jigon Jam'iyyar PDP Ya Bi Sahun Gwamnoni da Yan Majalisu, Ya Sauya Sheƙa Zuwa APC

Wani Jigon Jam'iyyar PDP Ya Bi Sahun Gwamnoni da Yan Majalisu, Ya Sauya Sheƙa Zuwa APC

  • Wani babban Jigon jam'iyyar adawa PDP a jihar Imo ya fice daga jam'iyyar zuwa APC mai mulki
  • Mr Hillary Ugochukwu, ya ɗauki wannan matakin ne a wurin taron cin abinci da shugabannin APC suka shirya don girmama shi
  • Ya kuma yi kira ga masoyan sa da su mara masa baya domin bada gudummuwa ga cigaban jihar

Wani babban jigon PDP a jihar Imo, Mr Hillary Ugochukwu, ya sauya sheƙa zuwa jam'iyya mai mulki APC, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Da Tunanin Yan Najeriya a Zuciya Shugaba Buhari Yake Bacci, Gwamna

Ugochukwu, wanda tsohon ɗan takarar sanata ne ya bayyana matakin komawa APC ne a wurin wani taron cin abinci da shugabannin APC suka shirya don girmama shi.

Hakanan ya kuma yabawa gwamnan Imo, Hope Uzodinma, bisa nasarorin da gwamnatinsa ta samu tun shigarsa Ofis, ya kuma nuna sha'awar aiki tare domin kawo cigaba a Imo.

Tsohon ɗan takarar sanatan, kuma masanin harkar noma, ya yi kira ga ɗumbin masoyanshi da su biyo shi zuwa APC.

Jigon PDP a Imo ya sauya sheƙa zuwa APC
Wani Jigon Jam'iyyar PDP Ya Bi Sahun Gwamnoni da Yan Majalisu, Ya Sauya Sheƙa Zuwa APC Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Na yi rijista da jam'iyyar APC

Ugochukwu ya bayyana cewa ya riga ya yi rijista da jam'iyyar APC a gundumarsa Ugwa, ƙaramar hukumar Mbaitoli, jihar Imo, tun kafin ya bayyana kudirinsa a matakin jiha.

"Bayan dogon nazari da kuma tattaunawa, na yanke hukuncin sauya sheƙa zuwa jam'iyya mai mulki, domin samun damar bada gudummuwa ta a cigaban jihar mu da gwamna Hope Uzodimma ya ɗakko." inji shi.

KARANTA ANAN: Yan Bindiga Sun Kutsa Cikin Gida, Sun Yi Awom Gaba da Miji da Mata a Nasarawa

Babu kamae jam'iyyar APC

Da yake jawabi a wurin taron da ya gudana a sakateriyar APC dake Owerri, Mr Lemmy Akakem, jigon APC, ya bayyana matakin Ugochukwu na aiki tare da gwamnatin jihar a matsayin wata babbar alamar nasarar APC farat ɗaya.

Ya kuma yi kira ga sauran jiga-jigan siyasa a jihar da su yi ko yi da shi domin kawo cigaba a jihar Imo.

A wani labarin kuma Shugaba Buhari Ya Yi Martani Kan Harin Zamfara da Kaduna, Ya Umarci Dakarun Soji Su Murkushe Yan Ta'adda

Shugaba Buhari ya yi Allah wadai da hare-hare da aka kai kwanan nan jihar Zamfara da Kaduna.

Shugaban ya umarci sojoji da su ɗauki matakin murkushe duk wasu yan ta'adda ta yaren da zasu fahimta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel