Jerin Ministocin Buhari da Basu da Kwalin NYSC da Kuma Dalilan da Suka Jawo

Jerin Ministocin Buhari da Basu da Kwalin NYSC da Kuma Dalilan da Suka Jawo

Tsokacin Edita: Shin takardar NYSC ya kamata ta zama babbar jigo a aikin gwamnati ko da kuwa dan kasa na da cikakken kwarewa wajen ba kasa gudunmawar da zata ci gaba? Cece-kuce da ake yi game da takardar NYSC yasa Legit ta tattaro wasu daga cikin ministocin Buhari da basu da takardar NYSC, kuma suka yi aiki tukuru tare da ba kasa gudunmawa na gari.

Ana ta cece-kuce game da takardar NYSC na tsohuwar ministar kudi Kemi Adeosun, lamarin da ya kai ga ta mika takardar ajiye aiki a matsayinta na minista a shekarar 2018.

Mutane da dama sun kagu cewa, ta yiwu akwai wasu daga cikin jigogin gwamnatin Buhari da basu mallaki takardar NYSC ba, wannan yasa wannan rahoton na Legit.ng Hausa ya tattaro sunayen wasu ministocin Buhari da basu takardar da kuma dalilan da suka jawo haka.

KARANTA WANNAN: Daga Karshe: An Sanya Ranar Mukabala Tsakanin Abduljabbar Kabara da Malaman Kano

  1. Audu Ogbeh - Ba ya bukatar takardar shaidar NYSC saboda ya kammala karatu kafin a fara shirin NYSC a Najeriya.
Jerin Ministocin Buhari da Basu da Takardar NYSC da Kuma Dalilan da Suka Jawo
Audu Ogbeh | Hoto: businessday.ng
Asali: UGC

2. Osagie Ehanire - Mai shekaru 72. Lokacin da ya kammala karatu daga Jami'ar Ludwig Maximilian ta Munich a 1973, dokar NYSC ba ta aiki.

Jerin Ministocin Buhari da Basu da Takardar NYSC da Kuma Dalilan da Suka Jawo
Osagie Ehanire | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

3. Anthony Anwuka - Shi ma bai yi NYSC ba, saboda ya kammala karatu sa a Jami'ar Sierra Leone a 1974 kafin assasa NYSC.

Jerin Ministocin Buhari da Basu da Takardar NYSC da Kuma Dalilan da Suka Jawo
Anthony Anwuka | Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

4. Abdulrahman Dambazau - Bai yi NYSC ba, amma an bashi takardar dage NYSC saboda matsayinsa na jami’in soji a lokacin da ya kammala karatunsa daga Jami’ar Jihar Kent ta Amurka, yayin da yake kan aiki.

Jerin Ministocin Buhari da Basu da Takardar NYSC da Kuma Dalilan da Suka Jawo
Abdurrahman Danbazau | Hoto: businessday.ng
Asali: UGC

5. Mustapha Shehuri - Yayi karatun digirinsa na farko ne a shekarar 2007 lokacin yana da shekaru 46, daga Jami’ar Maiduguri. Saboda ya kammala karatunsa yana sama da shekaru 30, an ba shi takardar dage NYSC saboda yawan shekaru.

Jerin Ministocin Buhari da Basu da Takardar NYSC da Kuma Dalilan da Suka Jawo
Mustapha Shehuri | Hoto: sunnewsonline.com
Asali: UGC

6. Amina Mohammed - Ba ta da digiri na farko don haka ba ta bukatar NYSC.

Jerin Ministocin Buhari da Basu da Takardar NYSC da Kuma Dalilan da Suka Jawo
Amina Mohammed | Hoto: punchng.com
Asali: UGC

7. Hadi Sirika - Sirika bashi da takardar NYSC saboda ba shi da digiri na farko ko wata takarda makanciniyar haka, in ji Premium Times.

Jerin Ministocin Buhari da Basu da Takardar NYSC da Kuma Dalilan da Suka Jawo
Hadi Sirika | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Bayan da kotu ta wanke ta kan batun NYSC, ministar Buhari ta yi martani

Wata tsohuwar Ministar Kudi Misis Kemi Adeosun ta ce wata Babbar Kotun Tarayya dake Abuja ta tabbatar da gaskiyarta, The Nation ta ruwaito.

Amma duk da haka ta yarda da cewa ta yi matukar bakin ciki game da zarginta da gabatar da takardar NYSC ta bogi.

Ta ce hukuncin da Justis Taiwo Taiwo ya yanke ba nasara ce kawai gare ta kadai ba, nasara ce ga dukkan ‘yan Najeriya mazauna kasashen waje.

Ta ce za ta kara daukar matakai a lokacin da ya dace don kare mutuncinta.

KARANTA WANNAN: Jami'a a Najeriya ta ce dole dalibai su fara sanya 'Uniform', dalibai sun yi turjiya

Kotu ta wanke tsohuwar ministan Buhari kan badakalar kwalin NYSC

A wani labarin, Tsohuwar ministan kudi ta Najeriya, Kemi Adeosun a ranar Laraba, 7 ga watan Yuli ta wanku a gaban kotu kan zarginta da ake da kin yi hidimar kasa ta NYSC.

Kamar yadda alkali mai shari'a, Taiwo Taiwo na babbar kotun tarayya dake Abuja ya yanke, bai dace ta yi hidimar kasan ba koda ta kammala digiri a shekaru 22 saboda har a lokacin 'yar Birtaniya ce, The Nation ta ruwaito.

Kotun ta kara da cewa tsohuwar ministan ta dawo kasarta ta gado lokacin da ta wuce shekaru 3 a duniya, lamarin da yasa ba za ta iya hidimar kasa ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel