Jerin tambayoyin da aka jefawa Sheikh Abduljabbar Kabara da martanonin da ya bada

Jerin tambayoyin da aka jefawa Sheikh Abduljabbar Kabara da martanonin da ya bada

A ranar Asabar, 10 ga watan Yuli, 2021, aka tafka makabala tsakanin Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara da sauran malaman Kano kamar yadda aka shirya.

Malaman da su ka zauna da Abduljabbar Nasiru Kabara

Malaman da su ka zauna da shi sun hada da Dr. Rabiu Umar Rijiyar Lemu, Malam Abubakar Mai Madatai, Malam Kabir Bashir Kofar Wambai da Malam Mas’ud Hotoro.

Babban malamin nan kuma mataimakin sakartare na majalisar kolin addinin musulunci, Farfesa Salisu Shehu ne ya zama alkalin wannan tattauna wa da aka yi.

Kamar yadda BBC Hausa ta rahoto, da kimanin karfe 10:20 na safe aka shiga fafata wa tsakanin malaman inda Dr. Rabiu Umar Rijiyar Lemu ya jefa tambayar farko.

Rijiyar Lemu ya bukaci Abduljabbar Kabara ya warware maganar da ya yi na cewa akwai hadisin da ya nuna Manzon Allah SAW ya yi mai dakinsa, Safiyya RA, fyade.

An nemi Abduljabbar Kabara ya kawo wannan hadisin a littafin Sahih Bukhari, amma sai ya gagara yin hakan, ya ce bai dace a fara da jefo masa wannan tambaya ba.

Kara karanta wannan

Batanci ga Annabi: Tambuwal ya lallashi matasa a jihar Sakkwato, ya ce ana bincike kan mai laifin

Daga nan sai wakilin Izala, Kabir Bashir Kofar Wambai ya kunna sautin wani karatun Kabara, da ya ce wata mata ta zo gaban Manzon Allah SAW ta na yin kwarkwasa.

KU KARANTA: Ana mukabala tsakanin Malaman Kano da Abduljabbar Kabara

A nan Shehin Qadiriyyan ya ce ba ayi masa adalci ba, bai yi karin bayani a kan wannan mas’alar ba.

Abduljabbar Kabara ya ce Mukabala ta canza salo

Bayan nan sai Abduljabbar Kabara ya bukaci tattaunawar ta kasance kan mas’alolin da malaman da ke adawa da shi su ka kai gaban hukuma, kuma aka yarda da hakan.

Abduljabbar Kabara ya yarda ya yi kuskure da ya ce Manzon Allah SAW ya na tura wata mata domin ta gano masa al’aurar mata, amma ya yi kukan karancin lokaci.

A wajen wannan zama, Shehin ya yi ta korafin lokacin da aka ba shi ba za su isa ya yi bayani ba. Kabara ya ce karatun sa'a uku, ba zai maimatu a cikin mintuna goma ba.

Kara karanta wannan

AbdulJabbar da Malaman Kano: Bayan kimanin awanni 5, an kammala mukabalar

Kabir Bashir Kofar Wambai ya dauki lokaci ya fadakar da abokin zamansa ya rika fadan inda ya dauko maganganun da yake da’awa, a nan ma dai Shehin bai yi hakan ba.

Mas’ud Hotoro ya kalubalanci Kabara ya kawo inda aka kira Manzon Allah SAW da Bunsuru ko Bamaguje, sai ya ce mintuna goma sun yi kadan ya maida masa martani.

KU KARANTA: An sa ranar mukabala da Abduljabbar Kabara a Kano

Jerin tambayoyin da aka jefawa Sheikh Abduljabbar Kabara da martanonin da ya bada
Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara
Asali: Facebook

Sheikh Abubakar mai Madatai ya bijiro da karatun Abduljabbar Kabara inda ya ce an sha giya wajen auren Manzon Allah, inda shi kuma ya ce kare addini ne yake yi.

Daga nan sai Abubakar Madatai ya nemi Sheikh Abduljabbar Kabara ya janye kalamansa, amma abokin tattaunawarsa ya ce ya na kan bakarsa, ya nemi a sake yin zama.

A karshe Alkalin muqabalar ya ce Abduljabbar Nasiru Kabara bai iya amsa ko tambaya guda ba, sai dai ya buge da wala-wala. Kabara kuwa ya ce bai gamsu da zaman ba.

Kara karanta wannan

Yadda ya dace Musulmi ya fuskanci kwanaki goma (10) na farkon watan Zhul-Hijja, Daga Sheikh Umar Zaria

A baya an ji cewa shugaban malamai na arewa maso yamma, Sheikh Ibrahim Khalil, ya sanar da cewa kima da darajar Malam Abduljabbar Kabara bai kai ayi masa gayya ba.

Sheikh Ibrahim Khalil ya bayyana hakan ne yayin da ya yi wata tattaunawa da manema labarai.

Asali: Legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel