AbdulJabbar da Malaman Kano: Bayan kimanin awanni 5, an kammala mukabalar
- Alkalin mukabala ya yi jawabi hukuncinsa bayan sauraron bangarorin biyu
- Farfesa Salisu Shehu yanzu ya mika lamarin ga gwamnatin Kano ta yanke shawara
- A cewarsa, ko tambaya guda Malam AbdulJabbar bai amsa ba
Bayan kimanin awanni biyar ana tattaunawa kan maganganun da ake zargin Malam AbdulJabbar Kabara da yi, na kawo karshen zaman.
Bayan sauraron duka bangarorin biyu, Alkalin mukabalar, shugaban jami'ar Al-Istiqamah Farfesa Salisu Shehu ya ce babu tambayar da Abdul Jabbar ya amsa cikin tambayoyin da akayi masa.
Ya mika lamarin yanzu ga gwamnatin jihar Kano domin ta yanke shawararta.
Jawabin Alkalin Muqabar, Farfesa Salisu Shehu yace:
"A kowace gaba, duk tambayar da akayiwa Malam AbdulJabbar, ba ya tsayawa akan gabar da aka masa tambaya. Da farko yana cewa babu isasshen lokaci, na biyu yana cewa a tsayawa a kan maudu'i guda daya a yi magana amma shine idan ya tashi baya tsayawa a kan maudu'i guda daya, sai ya yi ta yawo maimakon amsa tambayoyin."
"Ni a gani na gaba daya babu wata amsa ko guda ɗaya, da Malam Abduljabbar ya amsa daga cikin tambayoyin da Malaman nan suka yi masa, don haka yanzu ya rage na Gwamnatin jihar Kano, ta san irin matakin da zata ɗauka."
DUBA NAN: Gwamnatin tarayya ta saki hotunan Fursunonin da suka gudu a Jos
KU DUBA: A tarihin Najeriya, babu gwamnatin ta taba jin kan talakawa irin ta Buhari, Gwamna Masari
Ga wadanda ke bukatar kallon mukabalar a talabijin, Diraktan tashar Sunnah TV, Sheikh Abu Aisha Ibrahim Disina yace za'a haska da daren Asabar, 10 ga Yuli, 2021.
Bayan tsawon lokaci, mukabala ta gudana
Bayan kai komo da aka yi kan batun mukabalar Sheikh Abduljabbar, an sanya ranar da za a caccaka tsinke tsakanin Sheikh Abduljabbar da malaman Kano
Malaman da suka kara da Malam AbdulJabbar sune akwai Ustaz Kabir Bashir Abdulhamid, Dr Muhammad Rabiu Rijiyan Lemo, Malam Mas'ud Hotoro, da Malam Abubakar Madatai.
Asali: Legit.ng