An kama miyagun da suka yi garkuwa da mahaifin tsohon gwamna a jihar Filato
- Rundunar 'yan sandan jihar Filato sun damke mutum takwas daga cikin wadanda suka sace mahaifin tsohon gwamna Joshua Dariye
- Ubah Gabriel, mai magana da yawun 'yan sandan jihar ya tabbatar da kamen a wani samamen hadin guiwa na jami'an tsaro a jihar
- Wannan ne karo na biyu da miyagu suka sace Chibi Dariye a kauyen Mushere dake karamar hukumar Bokkos ta jihar Filato
Bokkos, Filato
Mutum takwas 'yan kungiyar miyagu wanda suka sace mahaifin tsohon gwamnan jihar Filato, Joshua Chibi Dariye, sun shiga hannun jami'an tsaro a karamar hukumar Bokkos ta jihar Gombe.
Mai magana da yawun 'yan sandan jihar, Ubah Gabriel, wanda ya tabbatar da kamen ya ce masu garkuwa da mutanen sun shiga hannu ne yayin wani samamen hadin guiwa na jami'an tsaro da aka kai maboyarsu.
KU KARANTA: Lauretta Onochie: Ana caccakata ne saboda ina bin ka'idar aikina
KU KARANTA: Da duminsa: PSC ta hana Magu karin girma, ta bayyana umarnin wanda take jira
A shekarar da ta gabata aka sace Chibi Dariye
An yi garkuwa da Chibi Dariye a watan Yunin 2020 a kauyen Mushere dake Bokkos. Tun bayan nan, ba a san inda yake ba har sai makon da ya gabata yayin da aka kama masu garkuwa da mutanen.
Daily Trust ta ruwaito cewa wannan ne karo na biyu da aka sace Chibi Dariye a gidansa dake kauyen Mushere.
An taba sace shi a shekarar 2015 amma daga baya an sako shi bayan biyan kudin fansa ga masu garkuwa da mutane, Daily Trust ta wallafa.
A wani labari na daban, Ibrahim Magu, tsohon mukaddashin shugaban hukumar yaki da rashawa tare da hana yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, an zargesa da kange wasu bincike na zargin rashawa da ake wa wani gwamna mai ci yanzu da wasu tsoffin gwamnoni uku.
Kwamitin Jastis Ayo Salami ya ce yayin da Magu ke shugabantar EFCC, Magu "ya umarci jami'ai da kada su bincike" kan zargiin rashawa kan wasu mutum hudu, TheCable ta ruwaito.
Da dumi-dumi: Shugaban 'yan fashi ya kai hari kauyukan Zamfara, ya sace mutum 150 saboda an kama mahaifinsa
Tsoffin gwamnonin an gano sun hada da Rabiu Musa Kwankwaso na jihar Kano, Donald Duke na jihar Cross River da Ibikunle Amosun na jihar Ogun wanda yanzu haka sanata ne.
Asali: Legit.ng