Lauretta Onochie: Ana caccakata ne saboda ina bin ka'idar aikina

Lauretta Onochie: Ana caccakata ne saboda ina bin ka'idar aikina

  • Lauretta Onochie, mai bada shawara ta musamman ga shugaba Buhari tace ita 'yar ka'ida ce
  • Onochie ta sanar da majalisar dattawa cewa tsaurinta da bin ka'ida yasa ake caccakarta
  • Ta sanar da majalisar dattawa yayin tantance ta cewa bata da bangaranci ko kadan

Mai bada shawara ta musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai, Lauretta Onochie, ta ce ita ba 'yar siyasa bace amma tana bin ka'idojin aikinta ne a komai.

Ta sanar da hakan ne yayin jawabin farko yayin da ake tantanceta a matsayin kwamishinan kasa ta INEC a majalisar dattawa, Daily Trust ta ruwaito.

Ta ce, "Bani da jinin bangaranci. Na ga korafe-korafe daban-daban kan zabena da aka yi ba daga PDP ba kadai, har da wasu 'yan APC.

KU KARANTA: Da duminsa: 'Yan Boko Haram sun bindige mutum 18 a Adamawa

Lauretta Onochie: Ana caccakata ne saboda ina bin ka'idar aikina
Lauretta Onochie: Ana caccakata ne saboda ina bin ka'idar aikina. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

KU KARANTA: 2023: Zulum ya goyi bayan gwamnonin kudu kan mika mulki yankinsu

"Bana bangaranci, sun sani doka ce kawai nake bi. Babu wanda ya dace ya ji wani tsoro don an nada ni kwamishinan INEC mai wakiltar Delta. Abinda na sani shine, ni ina bin ka'idoji, shiyasa suke caccakata. Ina bin ka'ida kuma ina bin doka."

Ana cigaba da tantancewa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar 12 ga Oktoba ya zabi Onochie daga Delta, Farfesa Muhammad Sani Kalla daga Katsina, Farfesa Kunle Cornelius Ajayi daga Ekiti, Saidu Babura Ahmad daga Jigawa, Farfesa Sani Muhammad Adam daga arewa ta tsakiya da Dr Baba Bila daga arewa maso gabas a matsayin kwamishinonin hukumar zabe.

Zaben Onochie ya kawo cece-kuce daga 'yan majalisar adawa da kungiyoyi wadanda suka ce ta cika bangaranci, don haka bai dace ta zama kwamishinar wuri mai muhimmanci kamar INEC.

A makon da ya gabata, shugabannin PDP sun yi zanga-zangar lumana a majalisar dattawa inda take bukatar a yi watsi da zaben Onochie da Buhari ya yi.

A wani labari na daban, tsohuwar ministan kudi ta Najeriya, Kemi Adeosun a ranar Laraba, 7 ga watan Yuli ta wanku a gaban kotu kan zarginta da ake da kin yi hidimar kasa ta NYSC.

Kamar yadda alkali mai shari'a, Taiwo Taiwo na babbar kotun tarayya dake Abuja ya yanke, bai dace ta yi hidimar kasan ba koda ta kammala digiri a shekaru 22 saboda har a lokacin 'yar Birtaniya ce, The Nation ta ruwaito.

Kotun ta kara da cewa tsohuwar ministan ta dawo kasarta ta gado lokacin da ta wuce shekaru 30 a duniya, lamarin da yasa ba za ta iya hidimar kasa ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng