Iyayen daliban Bethel sun fusata, sun fatattaki kwamishinan El-Rufai a yankinsu

Iyayen daliban Bethel sun fusata, sun fatattaki kwamishinan El-Rufai a yankinsu

  • Wasu fusatattun iyaye sun fatattaki tawagar kwamishina a jihar Kaduna lokacin da ya ziyarce su
  • Iyaye sun yi wa kwamishinan ihu tare da kokarin korarsa a yankinsu, yayin da suke nuna fushinsu ga sace daliban Bethel
  • Jami'an tsaro sun yi kokarin kwantar da tarzomar, amma lamarin ya ci tura domin kuwa iyayen sun dage

Samuel Aruwan, Kwamishinan Tsaron Cikin Gida a Jihar Kaduna, ya hadu da fushin iyaye a ranar Litinin lokacin da ya ziyarci Karamar Hukumar Chikun ta Jihar Kaduna.

Kwamishinan ya jagoranci wata tawaga zuwa Maramara a cikin Karamar Hukumar don kan sace daliban Makarantar Sakandaren Betel da aka yi.

Daily Trust ta ruwaito yadda wasu mutane dauke da makamai suka kutsa cikin makarantar da safiyar ranar Litinin inda suka sace dalibai 121 yayin da suka kashe sojoji biyu.

KARANTA WANNAN: Da Duminsa: Ministar Buhari da ta yanki jiki ta fadi ta farfado, an sallame ta daga asibiti

Iyayen daliban Bethel sun fusata, sun fatattaki kwamishinan El-Rufai a yankinsu
Kwamishinan tsaro na cikin gida na jihar Kaduna | Hoto: worldlinknews.com.ng
Asali: UGC

Sa’o’i bayan faruwar lamarin, Aruwan ya ziyarci jama’ar yankin amma fusatattun iyaye da masu zanga-zanga suka tare ayarinsa suna masa ihu: "Ka koma! Ka koma! ”.

Jami'an tsaron dake tare da kwamishinan sun yi kokarin kwantar da hankalin masu zanga-zangar amma lamarin ya ci tura.

Yayin da ihun ya ci gaba, motocin dake cikin ayarin Aruwan sun juya baya daga wurin hakazalika mutane suka yi ta ihu baki daya.

Wasu mutane sun yiwa kwamishinan izgili kuma sun kafta tafi tare da nuna goyon baya ga iyayen da suka fusata.

Bethel Baptist:Ƴan bindiga sun nemi a basu shinkafa da wake da zasu ciyar da ɗalibai 121 da suka sace a Kaduna

Yan bindiga, wadanda suka kai hari Maraban Rido a karamar hukumar Chikun na jihar Kaduna a ranar Litinin suka sace wasu dalibai daga Bethel Baptist High School, Damishi, sun tuntubi masu makarantar suna neman kayan abinci, The Punch ta ruwaito.

Rahoton na The Punch ya ce yan bindigan sun nemi a basu kayan abinci irinsu Shinkafa, wake, kayan kanshi da mai domin su ciyar da daliban.

Wani ma'aikacin makarantar da ya nemi a boye sunansa, ya ce yan bindigan sun tabbatar da cewa dalibai 121 ne ke hanunsu.

A cewar wani babban jami'in makarantar, yan bindigan sun kira su a ranar Litinin sun kyale daya daga cikin daliban ya yi magana da wani ma'aikacin makarantar.

An gano cewa sun sake kira a ranar Talata sun kyalle daliban manyan aji na biyu, mace da namiji sunyi magana da wani babban jami'in makarantar.

Daliban manyan ajin sun tabbatar da cewa su 121 ne ke hannun masu garkuwar da mutane.

KARANTA WANNAN: Mafita: Matasan Katsina sun shirya horar da yadda za a fatattaki 'yan bindiga

'Yan Bindiga Sun Kashe Wani Ma'aikacin Fasa Dutse, Sun Yi Awon Gaba da Wani

A wani labarin, Wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu satar mutane ne sun kai hari a wani wurin fasa duwatsu a kauyen Ugya da ke karamar hukumar Toto a jihar Nasarawa, inda suka kashe wani ma’aikaci a wurin, Ibrahim Aliyu, tare da yin awon gaba da wani, Abdul Umar Ekuji.

Wani mazaunin yankin, mai suna Salihu ya ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 4:43 na yamma a ranar Litinin, Daily Trust ta ruwaito.

Wasu ‘yan bindiga dauke da bindigogin AK47 sun mamaye wurin da ake fasa duwatsun, wanda ya ce yana da nisan kilomita biyu da bainar jama’a.

Asali: Legit.ng

Online view pixel