Jami'a a Najeriya ta ce dole dalibai su fara sanya 'Uniform', dalibai sun yi turjiya

Jami'a a Najeriya ta ce dole dalibai su fara sanya 'Uniform', dalibai sun yi turjiya

  • Daliban jami'ar Neja Delta sun fusata, sun ce sam basu amince da shirin sanya tufafin makaranta ba
  • Sun bayyana kokensu yayin da suke gudanar da zanga-zangar lumana a harabar makarantar
  • Sun koka kan kudaden da aka sanya na tufafin, tare da cewa suna son a kori shugaban jami'ar

Daliban Jami’ar Neja Delta (NDU) mallakar jihar Bayelsa sun gudanar da zanga-zanga kan shirin da shugabannin makarantar ke yi na bullo da tsarin sanya tufafin makaranta da daliban za su biya, Daily Trust ta ruwaito.

Fiye da dalibai 20,000 ne suka gudanar da wata zanga-zangar lumana a cikin harabar makarantar dake tsibirin Wilberforce na Amassoma a karamar hukumar Kudancin Ijaw da ke jihar a ranar Talata.

Yayin zanga-zangar, daliban na kira ga gwamnatin jihar da ta tursasa shugabannin gudanarwar jami'ar da su janye shawarar da suka yanke a kansu.

KARANTA WANNAN: Iyayen daliban Bethel sun fusata, sun fatattaki kwamishinan El-Rufai a yankinsu

Jami'a a Najeriya ta ce dole dalibai su fara sanya 'Uniform', dalibai sun yi zanga-zanga
Jami'ar Neja Delta | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Sun kuma yi Allah wadai da batun hana ayyukan kungiyar dalibai a cikin makarantar, suna masu cewa hanin an yi shi ne don dakile koke-koke da kuma rufe kafar karbar kudade ga tsofaffin dalibai.

Daliban da suka fusata sun yi kira ga Gwamna Douye Diri da ya kori Shugaban Jami'ar, Farfesa Samuel Edoumiekumo wanda ke neman cika wa'adi na biyu, suna masu cewa manufofinsa abun dariya ne ga makarantar.

Wasu daga cikin daliban da suka nemi a sakaya sunayensu sun yi zargin cewa an umarci daliban injiniyanci da su biya kusan N30,000 kowannensu na tufafin karatunsu yayin da daliban wasu fannoni za su biya N20,000 kowanne.

A cewarsu:

“Gabatar da tufafin makarantar wata alama ce ta nuna fin karfi daga shugabannin makarantar da nuna zalunci a bayyane.

Shugabannin jami'ar sun yi ikirarin cewa batun sanya tufafin da ba su dace ba da dalibai mata ke yi shi ya sa aka bullo da tsarin tufafin makaranta a kan daliban, Vanguard ta ruwaito.

Jami'in Hulda da Jama'a na NDU, Idoni Indezi, lokacin da aka tuntube shi, ya ce shugabannin makarantar ba su kayyade kudin da za a sanya na tufafin makarantar ba kuma har yanzu ana ci gaba da tattaunawa a matakan sashe da na malamai.

KARANTA WANNAN: Da Duminsa: Ministar Buhari da ta yanki jiki ta fadi ta farfado, an sallame ta daga asibiti

Annobar Korona: An Garkame Wasu Makarantu Biyu Saboda Tsoron Ta'azzarar Korona

A wani labarin, An rufe wasu makarantu biyu masu zaman kansu a yankin Lekki da ke jihar Legas saboda tsoron barkewar annobar Korona. Makarantun da aka garkame su ne Lagoon Girls’ Secondary School da Standard Bearer School.

Legit.ng Hausa ta ruwaito daga jaridar The Nation cewa, ta samu labari daga wata majiya a Ofishin tabbatar da ingancin Ilimi, a Ma’aikatar Ilimi ta jihar Legas cewa an rufe makarantun ne bayan da suka kawo rahoton kansu ga ma’aikatar wanda ya kai ga jami’ai suka ziyarce su.

Majiyar ta ce:

#“Daga abin da na tattara, bana tsammanin ofishinmu ne ya gano makarantun. Makarantun ne suka ba da rahoton kansu. Ba iya samun magana da shugabannin tawagar da suka je wurin ba domin su ba ni cikakken bayanin abinda ya faru lokacin da suka isa wurin."

Asali: Legit.ng

Online view pixel