Da Dumi-Ɗumi: Wasu Yan Bindiga Sun Yi Awon Gaba da Shugaban Fulani, Jamhuro Sule
- Wasu yan bindiga sun yi awon gaba da shugaban fulani, Alhaji Usmanu Sule, yayin da yakai ziyara ƙauye
- Rahotanni sun bayyana cewa maharan sun kutsa har cikin gida kuma suka tafi da shi
- Mutumin da aka sace aka yi garkuwa da shi ɗan kimanin shekara 90 shine shugabam fulanin Jamhuro a Kwara
Yan bindiga sun yi awon gaba da wani sanannen shugaban Fulani, Alhaji Usmanu Sule, wanda aka fi sani da Jamhuro Lamba, a Lalate, karamar hukumar Ibarapa, jihar Oyo, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.
KARANTA ANAN: Ma'aikata 774,000: FG Ta Bayyana Abinda Take Shiryawa Ma'aikatan SPW Bayan Gama Biyansu N60,000
Wani mazaunin garin ya shaida wa manema labarai cewa an sace mutumin ɗan kimanin shekara 90 yayin da yaje ƙauye ziyartar yan uwansa.
Yace: "Yan bindigan sun mamaye ƙauyen inda suka yi awon gaba da shi, shine kaɗai babban mutum a wurin lokacin da suka zo. Kuma yana tare da mata da ƙananan yara a lokacin."
Asalin sunan Jamhuro
Abubakar Malam Buggol, wani mazaunin garin Lamba a jihar Kwara, ya shaidawa manema labarai cewa Jamhuro Usmanu Sule, shine shugaban fulanin Jamhuro na jihar Kwara.
Yace ana laƙabawa shugaban Fulani suna 'Jamhuro' idan yana zaune a yankin yarbawa na tsawon lokaci.
Yace: "Kamar yadda muke da Harɗo a matsayin sarkin fulani a arewa, haka muke da Jamhuro a matsayin sarkin fulanin dake zaune a kudu-yamma da kuma Kwara."
Boggol ya ƙara da cewa 'yayan wanda aka ɗauke basa gida yayin da yan bindigan suka kawo hari.
KARANTA ANAN: Da Ɗuminsa: Sanatoci Sun Amince da Buƙatar Shugaba Buhari Na Sake Karɓo Bashin Tiriliyan N2.3tr
Hukumar yan sanda ba tace komai ba
Da aka tuntuɓe shi domin ya tofa albarkacin bakinsa, DSP Oseifo Adewale, kakakin hukumar yan sandan jihar Oyo, ya nemi a tura mai saƙo ne domin ya cikin taro.
Amma tun daga wannan lokacin bai dawo da amsar saƙon ba kuma bai amsa kiran wayar da aka ƙara masa ba.
A wani labarin kuma Majalisar Dokoki Zata Maida Gidajen Kallon Silma Zuwa Makarantun Islamiyya
Majalisar dokokin jihar Katsina zata mayad da gidajen kallon talabijin zuwa makarantun islamiyya.
Hon. Mustapha Jibia, shine ya gabatar da wannan kudurin a gaban majalisar a zaman ta na ranar Talata.
Asali: Legit.ng