Da Ɗuminsa: Sanatoci Sun Amince da Buƙatar Shugaba Buhari Na Sake Karɓo Bashin Tiriliyan N2.3tr

Da Ɗuminsa: Sanatoci Sun Amince da Buƙatar Shugaba Buhari Na Sake Karɓo Bashin Tiriliyan N2.3tr

  • Sanatoci sun amince da buƙatar shugaba Buhari na sake karɓo bashin kuɗi kimanin 2.3 tiriliyan
  • A watan Mayun da ya gaba ta ne, Buhari ya nemi amincewar majalisa kan sake karɓo bashin
  • Sanatocin sun umarci ministan kuɗi, kasafin kuɗi da tsare-tsaren ƙasa da Gwamnan CBN su kawo musu takardar bayani kan lamarin

Majalisar dattijai, a ranar Laraba, ta amince da buƙatar shugaban ƙasa Muhammadu Buhari, na karɓo bashin tiriliyan N2.3tr domin cike giɓin kasafin kuɗin 2021, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Dokar Hana Makiyaya Kiwo a Fili Ba Zata Yi Aiki Ba, Inji Gwamna Zulum, Ya Faɗi Dalili

Amincewar ta biyo bayan nazari da sanatocin suka yi a kan rahoton kwamitin dake kula da bashin da ake bin Najeriya a gida da waje, wanda Sanata Clifford Ordia (PDP, Edo), yake jagoranta, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

Sanatocin sun amince da buƙatar shugaba Buhari na fitar da yuro biliyan $3b amma kada ya wuce $6.1 billion a kasuwar duniya domin aiwatar da giɓin kasafin kuɗi na 2.3 tiriliyan.

Zauren majalisar dattijai ta Najeriya
Da Ɗuminsa: Sanatoci Sun Amince da Buƙatar Shugaba Buhari Na Sake Karɓo Bashin Tiriliyan N2.3tr Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Hakanan kuma sanatocin sun umarci ƙusoshin FG da abun ya shafa su kaiwa majalisa takardar dake ƙunshe da yawan kuɗin Amurka da aka samar da waɗanda suka karɓa bisa amincewa da amso wannan bashin da kuma yadda ake hada-hadar kuɗin a kasuwa.

A watan Mayu Shugaba Buhari ya nemi amincewarsu

A watan Mayun da ya gabata ne, shugaba Buhari ya nemi amincewar yan majalisa wajen samar da wasu kuɗaɗe daga ɓangarori da dama.

KARANTA ANAN: Majalisar Dokoki Zata Maida Gidajen Kallon Silma Zuwa Makarantun Islamiyya

"Mun yi ƙiyasin cewa Najeriya zata iya samar da $3 biliyan ko sama da haka, amma ba zai wuce $6.183 biliyan ba a cikin shekara 5 zuwa 30 masu zuwa," inji Buhari.

A wani labarin kuma Yan Bindigan da Suka Sace Ɗalibai a Kaduna Sun Kira Makarantar Ta Wayar Salula

Yan bindigan da suka sace ɗalibai a makarantar sakandiren Bethel Baptist, jihar Kaduna sun tabbatar da cewa sun sace ɗalibai 121.

Shugabam makarantar Bethel Baptist dake Kaduna, Rev. Yahaya Adamu Jangado, shine ya bayyana haka ga manema labarai ranar Talata.

Asali: Legit.ng

Online view pixel