Majalisar Dokoki Zata Maida Gidajen Kallon Silma Zuwa Makarantun Islamiyya

Majalisar Dokoki Zata Maida Gidajen Kallon Silma Zuwa Makarantun Islamiyya

  • Majalisar dokokin jihar Katsina zata mayad da gidajen kallon talabijin zuwa makarantun islamiyya
  • Hon. Mustapha Jibia, shine ya gabatar da wannan kudurin a gaban majalisar a zaman ta na ranar Talata
  • Majalisar ta baiwa kwamitocin ta umarnin gudanar da bincike kan gidajen kallon cikin watanni uku

Majalisar dokokin jihar Katsina ta fara karatu a kan wani ƙuduri dake neman a maida gidajen kallon talabijin dake faɗin kananan hukumomin jihar 34 zuwa makarantun islamiyya, kamar yadda the cable ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Shugaban Masallacin Sultan Bello Kaduna Ya Rigamu Gidan Gaskiya

Mustapha Yusuf Jibia, mai wakiltar mazaɓar jibiya a majalisar, shine ya gabatar da kudirin a zaman yan majalisun na ranar Talata, wanda kakakin majalisar, Tasi'u Mai Gari, ya jagoranta.

Yusuf Jibia ya bayyana cewa ɗaukar wannan mataki kusan ya zama wajibi saboda makarantun sun fi amfani ga al'umma fiye da kallon da ake yi.

Gidan Kallo Silma
Majalisar Dokoki Zata Maida Cibiyoyin Kallo 'Cinima' Zuwa Makarantun Islamiyya Hoto: premium times facebook
Asali: Facebook

A rahoton premium times, Hon. Yusuf ya ƙara da cewa ilimin addinin musulunci ya zama koma baya a mafi yawancin yankuna musamman karkara.

Yace idan aka amince da wannan kuduri, to zai taimaka wajen rage ƙalubalen tsaro da jihar Katsina take fama da shi.

A jawabinsa yace: "Idan aka amince da wannan kudurin, zai taimaka wajen rage yawan almajirai dake gararamba a kan hanya da sunan bara."

"Wasu daga cikin gidajen kallon an yi watsi da su, an mayar dasu bola, maɓoyar yan ta'adda da kuma wuraren da matasa marasa amfani suke zama."

Ƙudirin zai samar da aikin yi

Yusuf Jibia ya ƙara da cewa idan aka maida waɗannan wurare makarantun islamiyya, gwamnati zata ɗauki malaman da zasu koyar a makarantun, kuma hakan zai rage rashin aikin yi.

"Bawai gwamnati kaɗai ba, ɗai-ɗaikun mutane masu arziki dake kishin jihar zasu ɗauki mutane aiki a makarantun," inji shi.

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Yan Bindigan da Suka Sace Ɗalibai a Kaduna Sun Kira Makarantar Ta Wayar Salula

Majalisa ta miƙa kudirin ga kwamitoci

Bayan tattaunawa a kan kudurin, majalisa ta umarcin kwamitin addinai da na cigaban jama'a da su yi nazara akan lamarin.

Hakanan kuma, majalisar ta umarci kwamitocin biyu su binciko adadin waɗannan cibiyoyi da kuma adadin makarantun islamiyyan da basu aiki a faɗin jihar, su kawo rahoto cikin watanni uku.

A wani labarin kuma Yan Bindiga Sun Kutsa Kai Wata Sananniyar Kasuwa, Sun Yi Awon Gaba da Kayan Masarufi da Dama

Yan bindiga sun kai hari wani sananne kuma baban kanti 'supermarket' mai suna "Uzorbest Super-market Limited," dake Onu Asata, jihar Enugu.

Rahotanni sun bayyana cewa yan bindigan ba su cutar da kowa ba amma sun yi awon gaba da kayan masarufi.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel