Ma'aikata 774,000: FG Ta Bayyana Abinda Take Shiryawa Ma'aikatan SPW Bayan Gama Biyansu N60,000

Ma'aikata 774,000: FG Ta Bayyana Abinda Take Shiryawa Ma'aikatan SPW Bayan Gama Biyansu N60,000

  • Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa zata shirya wa ma'aikatan SPW horo na musamman a kan ƙananan sana'o'i
  • Gwamnatin tace zata shirya wannan bayad da horon ne a kowace mazaɓar sanata dake faɗin ƙasar nan
  • A cewar gwamnatin, tana fatan dukkan wanda ya amfana da wannan shirin ya zama mai dogaro da kansa nan gaba

Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa zata shirya wa yan Najeriya 774,000 waɗanda suka yi aikin gayya na shirin SPW horon yadda zasu kama sana'a da kuɗinsu na watanni uku N60,000, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Da Ɗuminsa: Sanatoci Sun Amince da Buƙatar Shugaba Buhari Na Sake Karɓo Bashin Tiriliyan N2.3tr

Kakakin hukumar NDE, Edmund Onwuliri, shine ya bayyana haka a wani jawabi da ya fitar ranar Laraba.

Yace horon da za'a baiwa ma'aiktan SPW wani ɓangare ne da shirin tsame su daga shirin, wanda suka kwashe wata uku, kamar yadda the nation ta ruwaito.

Onwuliri, bai bayyana adadin kuɗaɗen da za'a kashe wajen gudanar da wannan shirin ba, amma ya bayyana cewa bayar da horon sana'o'in zai gudana ne a kowace mazaɓar ɗan majlisar dattijai.

Ma'aikatan SPW
Ma'aikata 774,000: FG Ta Bayyana Abinda Take Shiryawa Ma'aikatan SPW Bayan Gama Biyansu N60,000 Hoto: nde.gov.ng
Asali: UGC

A cewarsa, ma'aikatan zasu amfana da dabarun yadda zasu ƙirƙiri sana'a bayan an tsame su daga shirin SPW.

Yace: "Bayan kammala ayyukan da shirin SPW ya ƙunsa kamar tsaftace wurare masu muhimmanci a yankunansu, an biya ma'aikatan naira N20,000 a kowane wata har tsawon wata uku kamar yadda aka tsara."

"Muna fatan wannan bada horo kan ƙananan sana'o'in zai taimakawa mutum 1,000 da aka ɗauka a kowace ƙaramar hukuma su tashi daga masu zaman kashe wando zuwa masu dogaro da kansu."

KARANTA ANAN: Babbar Magana: Jam'iyyar APC Zata Ladaftar da Ministan Buhari Saboda Cece-Kuce da Gwamna

Har yanzun akwai ma'aikatan SPW da ba'a biya su hakkinsu ba

Legit.ng hausa ta gano cewa wasu yan Najeriyan da suka gudanar da wannan aikin ba'a biya su haƙƙinsu kamar yadda aka baiwa sauran ba.

Shirin SPW ya gudana ne ƙarƙashin ma'aikatar ƙwadugo da samar da aikin yi ta hanyar hukumar samar da aikin yi ta ƙasa NDE.

A wani labarin kuma Dokar Hana Makiyaya Kiwo a Fili Ba Zata Yi Aiki Ba, Inji Gwamna Zulum, Ya Faɗi Dalili

Gwamna Zulum na jihar Borno, yace dokar hana fulani makiyaya kiwo a fili ba za ta yi aiki ba.

Gwamnan yace abinda ya kamata a maida hankali akai shine lalubo hanyar magance matsalar tsaro da ta abinci.

Asali: Legit.ng

Online view pixel