Babbar Magana: Jam'iyyar APC Zata Ladaftar da Ministan Buhari Saboda Cece-Kuce da Gwamna

Babbar Magana: Jam'iyyar APC Zata Ladaftar da Ministan Buhari Saboda Cece-Kuce da Gwamna

  • Jam'iyyar APC ta bayyana cewa zata duba abinda ministan yaɗa labarai, Lai Muhammed, ya yi domin hukunta shi
  • Shugaban kwamitin riƙo na APC ta Kwara, Abdullahi Samari Abubakar, yace za'a gudanar da bincike
  • Sanatocin dake wakiltar jihar Kwara a majalisar tarayya sun nuna goyon bayansu ga gwamna AbdulRazaq

Shugaban kwamitin riƙo na jam'iyyar APC reshen jihar Kwara, Abdullahi Samari Abubakar, yace za'a ɗauki matakin ladabtarwa a kan ministan yaɗa labarai, Lai Muhammed, kamar yadda the cable ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Da Ɗuminsa: Sanatoci Sun Amince da Buƙatar Shugaba Buhari Na Sake Karɓo Bashin Tiriliyan N2.3tr

Da yake fira da manema labarai a sakateriyar APC ta ƙasa dake Abuja, Abubakar ya bayyana cewa doka zata yi aiki akan ministan matuƙar aka tabbatar da ya yi wani laifi, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

Gwamnan Kwara da Ministan Yaɗa labarai
Babbar Magana: Jam'iyyar APC Zata Ladaftar da Ministan Buhari Saboda Cece-Kuce da Gwamna Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

Yace: "Har yanzun ministan ɗan jam'iyyar APC ne domin bai shaida mana ya fice daga jam'iyyar a hukumance ba, kuma bana tsammanin zai yi haka."

"Bana tunanin zai fice daga APC, amma dangane da abinda yayi mara daɗi, jam'iyyar mu na da ƙa'idoji da dokoki a kan kowane abu da ya taso."

"Idan muka gano maganar da yayi a fili babu ɗa'a a ciki ko kuma ta jawo rabuwar kai a cikin jam'iyyar APC, to maganar gaskiya zamu tabbatar doka ta yi aiki akan shi kamar yadda zata yi aiki a kan kowane mutum."

Da aka tambayeshi ko za'a iya dakatar da ministan, Abubakar yace idan abinda yayi ya kai a dakatar da shi "tabbas doka zata hau kansa."

KARANTA ANAN: Dokar Hana Makiyaya Kiwo a Fili Ba Zata Yi Aiki Ba, Inji Gwamna Zulum, Ya Faɗi Dalili

Sanatocin jihar sun goyi bayan gwamna

Sanatocin dake wakiltar jihar Kwara sun nuna goyon bayan su ga gwamnan jihar, AbdulRazaq AbdulRahman.

Umar Sadiq, sanatan dake wakiltar Kwara ta arewa, Lola Ashiru mai wakiltar Kwara ra kudu, da kuma Ibrahim Oleriegbe, mai wakiltar Kwara ta tsakiya, sun haɗu sun yi magana da manema labarai a Abuja.

Da yake jawabi kan ikirarin ministan, Umar Sadiq, yace gwamna ne ya samar musu da kuɗin da suka yi amfani da shi wajen yaƙin neman zaɓe.

A wani labarin kuma Majalisar Dokoki Zata Maida Gidajen Kallon Silma Zuwa Makarantun Islamiyya

Majalisar dokokin jihar Katsina zata mayad da gidajen kallon talabijin zuwa makarantun islamiyya.

Hon. Mustapha Jibia, shine ya gabatar da wannan kudurin a gaban majalisar a zaman ta na ranar Talata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262