Dokar Hana Makiyaya Kiwo a Fili Ba Zata Yi Aiki Ba, Inji Gwamna Zulum, Ya Faɗi Dalili

Dokar Hana Makiyaya Kiwo a Fili Ba Zata Yi Aiki Ba, Inji Gwamna Zulum, Ya Faɗi Dalili

  • Gwamna Zulum na jihar Borno, yace dokar hana fulani makiyaya kiwo a fili ba za ta yi aiki ba
  • Gwamnan yace abinda ya kamata a maida hankali akai shine lalubo hanyar magance matsalar tsaro da ta abinci
  • Zulum ya koka kan cewa har yanzun akwai kayan aikin sojoji da suka shekara 40 kuma ana amfani dasu a yanzun

Gwamnan Borno, Babagana Zulum, yace hana makiyaya kiwo a fili a wasu jihohin ƙasar nan ba zai yi aiki ba har sai an magance matsalar tsaro, kamar yadda punch ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Majalisar Dokoki Zata Maida Gidajen Kallon Silma Zuwa Makarantun Islamiyya

Gwamnan ya faɗi hakane a wata fira da yayi da gidan talabijin na Channels tv, a cikin shirin 'Sunrice Daily'

Mafi yawancin jihohin Najeriya da suka haɗa da jihohi 17 na kudancin ƙasar nan sun hana makiyaya kiwo a fili a yankunan su.

Gwamnan Borno, Babagana Zulum
Dokar Hana Makiyaya Kiwo a Fili Ba Zata Yi Aiki Ba, Inji Gwamna Zulum, Ya Faɗi Dalili Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Amma da yake jawabi a cikin shirin, Gwamnan jihar Borno yace matuƙar ana son dokar ta yi aiki dole sai amfara lalubo hanyar magance matsalolin tsaro da rikice-rikicen da ake fama da su a ƙasar nan, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

Zulum, yace: "Abun da ya kamata mu fara yi shine magance matsalolin tsaro da tattalin arziƙi da ayyukan ta'addanci ya jefa mu a ciki, shine yafi amfani a yanzun saboda ƙaruwar talauci a yankunan mu, domin shike ƙara rura wutar ta'addanci."

"Akwai ƙaruwar matsalar abinci, kuma wannan matsalar tafi ta'addanci hatsari. Shiyasa gwamnatin jihar Borno ta maida hankali wajen bayar da shawarwari dangane da noma a shekara 2 da suka gabata, ya kamata a bar manoma su je gonakinsu."

Sojoji basu da cikakkun kayan aiki

Zulum, wanda ya bayyana cewa zaman lafiya ya fara dawowa yankin Arewa maso gabas bayan shekara 11 ana yaƙi da Boko Haram, ya koka kan cewa jami'an soji basu da isassun makamai, jiragen yaƙi da kuma ƙarfin guiwar yaƙar yan ta'adda.

Yace: "Sojojin Najeriya na shekara 30 zuwa 40 da suka gabata, ba dai-dai suke da sojojin mu na yanzun ba."

"Abun takaici ne matuƙa, ya kamata ace mun wuce inda muke a yanzun wajen cigaba, amma idan kaduba zakaga makaman da suka shekara 40 ana amfani da su har yanzun."

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Yan Bindigan da Suka Sace Ɗalibai a Kaduna Sun Kira Makarantar Ta Wayar Salula

"Eh, shugaban ƙasa ya siyo makamai, amma yaushe zasu ƙariso Najeriya, wannan shine abin damuwar, amma ya kamata mu magance wannan matsalar cikin ƙanƙanin lokaci."

A wani labarin kuma Shugaban Masallacin Sultan Bello Kaduna Ya Rigamu Gidan Gaskiya

Shugaban masallacin Sultan Bello dake cikin Kaduna, Alhaji Sa'idu Kakangi ya riga mu gidan gaskiya.

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mukhtar Ramalan Yero, ya halarci sallar jana'iza da a ka gudanar a harabar masallacin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel