Mafita: Matasan Katsina sun shirya horar da yadda za a fatattaki 'yan bindiga

Mafita: Matasan Katsina sun shirya horar da yadda za a fatattaki 'yan bindiga

  • Matasa a jihar Katsina sun fara koyar wa kansu hanyoyin da zasu kare kansu daga 'yan bindiga
  • An gano cewa, wata kungiyar matasa ta dauki kudurin koyawa mazauna jihar amfani da bakan danko don kare kai
  • Matasan sun ce, tun da an basu damar kare kansu, to lallai sun samo hanya kuma za su tabbatar da hakan

Matasa a jihar Katsina sun shirya wani horo kan yadda ake amfani da bakan danko don yakar hare-haren da ‘yan bindiga ke kaiwa a jihar, The Cable ta ruwaito.

An sha samun hare-hare da dama daga ’yan bindiga a kan al’umomin da ke jihohin arewa, wanda ke haifar da sace-sacen mutane da kashe-kashe da dama.

Matasan, wadanda suka bayyana kansu a matsayin mambobin kungiyar sada zumunta ta jam'iyyar PDP a jihar Katsina, sun ce an shirya horon ne domin kare mazauna yankin daga barnar ‘yan bindiga.

KARANTA WANNAN: Ghali Na'Abba Ya Yi Martani Kan Kame Nnamdi Kanu da Farautar Sunday Igboho

Mafita: Matasan Katsina sun shirya horar da yadda za a fatattaki 'yan bindiga
Lokacin gudanar da atisayen | Hoto: thecable.ng
Asali: UGC

Matasan sun sanya wa atisayan horon ‘Atisayen Harbi da Bakan Danko’.

An ce matasan sun samar da bakan danko ne bayan shawarar da gwamnatin jihar ta bayar kwanan nan ga mazauna yankin da su dauki matakin da ya dace kan 'yan bindiga.

Gwamna Masari ya shawarci mazauna Katsina su fatattaki 'yan bindiga da kansu

Aminu Masari, gwamnan Katsina, ya bayyana a ranar 25 ga Yuni, lokacin da yake kaddamar da ayyukan tsaro da cibiyar kula da sadarwa a hedkwatar 'yan sanda, ya shawarci mazauna da su dauki mataki da nauyin tsare kawunansu.

Da yake magana a kan atisayen, wanda aka yada a shafukan sada zumunta, Nuraddeen Adam, shugaban kungiyar PDP ta kafofin sada zumunta a jihar, ya ce matasan sun yanke shawarar iawatar da horon ne domin kare kansu.

An kuma rarraba bakan danko ga mahalarta yayin atisayen, wanda aka ce ya gudana a ranar Litinin din da ta gabata.

Legit.ng Hausa ta bi diddigin Nurudeen Adam, kuma ta samo in da ya rubuta a shafinsa na Facebook cewa:

"Zamu cigaba da koyan hanyar kare kanmu tunda bamu iya cizo ko yakushi zamu sayi bakan danko domin kare kanmu daga masu kashe jama'a da kuma neman kudin fansa, Allah ka karemu amin."

KARANTA WANNAN: Shugaba Buhari ya jinjina wa jami'an tsaro bisa kame Nnamdi Kanu da farautar Igboho

Saura Kiris a Cimma Kudurin Haramta Barace-Barace a Jihar Katsina

A wani labarin, Kudurin dokar dake neman haramta bara a kan tituna a jihar Katsina ya zarce karatu na biyu a zauren majakisar jihar a ranar Litinin da ta gabata, Punch ta ruwaito.

Kudurin dokar zartarwa na neman sanya daurin shekara hudu ko zabin biyan tarar N10,000 ga wadanda suka karya dokar a farko, yayin da a karo na biyu za a dawo da mutum asalin jiharsa ko karamar hukumarsa.

Kudirin idan ya zama doka, ya kuma ba da damar korar duk wani mabaracin titi da ba dan Najeriya, zuwa kasarsa.

Kudirin wanda ya samo asali daga Gwamna Aminu Masari, an fara karanta shi a gaban majalisar ne a ranar 30 ga watan Yuni, 2021 daga Shugaban masu rinjaye, Abubakar Abukur.

Asali: Legit.ng

Online view pixel