Shugaba Buhari ya jinjina wa jami'an tsaro bisa kame Nnamdi Kanu da farautar Igboho
- Fadar shugaban kasa ta yabawa jami'an tsaron Najeriya bisa namijin aikin kamo Nnamdi Kanu
- Hakazalika ta jinjina musu bisa kai hari gidan dan rajin kare hakkin Yarbawa Sunday Igboho
- Ta kuma a karshe bayyana cewa, gwamnatin Buhari ba za ta amince da rarraba kan Najeriya ba
Fadar shugaban kasa ta jinjinawa hukumomin tsaron Najeriya game da kamun Nnamdi Kanu, shugaban kungiyar IPOB, da harin da aka kai kwanan nan a gidan Sunday Igboho, dan rajin kare hakkin Yarbawa da ke Ibadan.
A cikin wata sanarwa da ta fito ta hannun mai taimaka wa shugaban kan harkokin yada labarai, Garba Shehu, fadar shugaban kasar ta kuma yaba wa hukumomin kasashen duniya wadanda suka ba da hadin gwiwarsu ga hukumar bincike ta kasa (NIA) har aka kamo Kanu.
Rahoton ya kara da cewa IPOB, karkashin jagorancin dan yankin kudu maso gabas da ya ke fafutukar ballewa, ta zama kungiyar da ta yi kaurin suna wajen aikata kisan kai da maganganun batanci wadanda za su iya ruruta wutar fitina a Najeriya, jaridar Nigerian Tribune ta ruwaito.
KARANTA WANNAN: 'Yan Bindiga Sun Kashe Wani Ma'aikacin Fasa Dutse, Sun Yi Awon Gaba da Wani
Kungiyar IPOB ta jawo asarar rayuka da dunkiyoyi
Sanarwar ta yi nuni da cewa tashin hankalin da kungiyar ta haifar ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama da kuma lalata dukiyoyin jama'a wanda galibinsu mallakin gwamnati karkashin hukumonin 'yan sanda ne da na INEC.
Ya ce:
"Gwamnati ta dade tana lura da ayyukan kungiyar IPOB kuma tana da dalili mai karfi na gaskata cewa tushen kudadensu sun hada da kudaden da ake zargi an samesu ta hanyar aikata laifuka kuma ba bisa ka'ida ba.
"Dalilin wannan aiki daya tilo na jami'an tsaronmu, natsuwa, kwanciyar hankali da zaman lafiya ya dawo ga al'ummominmu wadanda a baya suke rayuwa cikin fargaba a koda yaushe game da wadannan bata gari."
Dalilin da yasa jami'an tsaro suka mamaye gidan Sunday Igboho
A kan dalilin da ya sa jami'an na 'yan sanda na farin kaya (DSS) suka mamaye gidan mai fafutukar kare hakkin Yarbawa Sunday Igboho, fadar shugaban kasa ta kara da cewa kalaman da Igboho ya yi sun zama masu cutarwa, "kalamai ne na nuna kyama da munanan".
PM News ta ruwaito cewa, gwamnatin da shugaba Buhari ke jagoranta ta bayyana karara cewa duk da cewa :
"Tana mutunta hakkokin 'yan kasa na bayyana ra'ayoyinsu kuma ta yarda da hakan a matsayin tsarin dimokiradiyya ... duk wani yunkuri na gina wajen adana makamai tare da tsare-tsare ko dabara ko kuma bayyana karara don lalata hadin kanmu ba za a lamunci hakan ba"
KARANTA WANNAN: Batun Daukaka Magu: PDP ta zargi shugaba Buhari da goyon bayan cin hanci da rashawa
Ghali Na'Abba Ya Yi Martani Kan Kame Nnamdi Kanu da Farautar Sunday Igboho
A wani labarin, Ghali Na’Abba, tsohon kakakin majalisar wakilai, ya ce yana goyon bayan matakin da gwamnatin tarayya ta dauka a kan Nnamdi Kanu, shugaban kungiyar IPOB da kuma Sunday Igboho, dan gwagwarmayar kafa kasar Yarbawa, The Cable ta ruwaito.
Na’abba, wanda shine shugaban kungiyar tuntuba ta Najeriya (NCFront), ya fadi hakan ne a matsayin martani ga wata sanarwa daga Olawale Okunniyi, sakataren kungiyar.
Okunniyi ya ce NCFront za ta kare Yarbawa masu zanga-zanga a kotu, biyo bayan kame wasu adadi na masu zanga-zangar a karshen mako a jihar Legas.
Asali: Legit.ng