Saura Kiris a Cimma Kudurin Haramta Barace-Barace a Jihar Katsina
- Wani kudurin dake kokarin hana barace-barace a jihar Katsina tuni ya zarce zama na biyu a majalisa
- An gabatar da kudurin ne da nufin inganta harkar Almajiranci da Tsangaya a fadin jihar ta Katsina
- An mika kudurin ga wani kwamiti domin tabbatar da kawo rahoton da ya dace kafin ci gaba da tattaunawa a kai
Kudurin dokar dake neman haramta bara a kan tituna a jihar Katsina ya zarce karatu na biyu a zauren majakisar jihar a ranar Litinin da ta gabata, Punch ta ruwaito.
Kudurin dokar zartarwa na neman sanya daurin shekara hudu ko zabin biyan tarar N10,000 ga wadanda suka karya dokar a farko, yayin da a karo na biyu za a dawo da mutum asalin jiharsa ko karamar hukumarsa.
Kudirin idan ya zama doka, ya kuma ba da damar korar duk wani mabaracin titi da ba dan Najeriya, zuwa kasarsa.
Kudirin wanda ya samo asali daga Gwamna Aminu Masari, an fara karanta shi a gaban majalisar ne a ranar 30 ga watan Yuni, 2021 daga Shugaban masu rinjaye, Abubakar Abukur.
KARANTA WANNAN: Soyayyar Facebook: Ma'auratan da suka hadu a Facebook, sun bayyana yadda suka fara
Mista Abukur ya bayyana cewa kudirin ya nemi tallafawa kokarin da gwamnatin jihar ke yi na dawo da Almajirai zuwa jihohinsu tare da tsabtace tsarin ilimin Tsangaya, Daily Nigerian ta ruwaito.
Manufar gabatar da kudurin
A cewarsa, idan har aka zartar da kudirin, zai taimaka wajen magance matsalar barace-barace a kan tituna.
Ya bayyana cewa yawancin yaran da ke yawo kan tituna sukan girma su zama barazana ga tsaron kasa.
Kudirin ya zarce zama na biyu, biyo bayan jerin shawarwari da 'yan majalisar suka yi yayin zaman majalisar wanda Kakakin Majalisar, Tasi’u Maigari ya jagoranta.
Mista Maigari ya ce mambobin majalisar za su ci gaba da tattaunawa kan kudirin saboda mahimmancinsa ga ci gaban jihar.
Rahotanni sun ce, an gabatar da kudirin ga kwamitin hadin gwiwa kan harkokin addini da ci gaban al’umma, tare da ba su wa’adin makonni shida don gabatar da rahoto a kan batun.
KARANTA WANNAN: Karin Bayani: Gwamnonin Kudu sun ce basu amince a sake kame wani a yankinsu ba sai da izininsu
Masari ya haramta bara a Katsina, ya yi wa islamiyoyi gargadi
A wani labarin, a shekarar da ta gabata, Gwamnatin Jihar Katsina ta hana barace-barace a fadin jihar kana ta yi wa makarantun allo da na islamiyya da ke jihar kashedin cewa har yanzu ba a basu damar cigaba da karatu ba.
Gwamnatin ta ce sassauta dokar kulle a jihar bai bayar da damar bude makarantu domin cigaba da karatu a cikinsu ba.
Sakataren gwamnatin jihar, Dr Mustapha Inuwa a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis ya ce an cimma zartar da wadannan matakan ne bayan bita kan halin da jihar ke ciki yayin wani taro
Taron ya samu hallarcin wakilan gwamnati, hukumomin tsaro, malaman addinin musulunci, shugabannin addini da mambobin kwamitin kar ta kwana na yaki da coronavirus na jihar.
Asali: Legit.ng