Bayan Shekara 245 da Samun Yanci, Shugaba Buhari Ya Aike da Saƙon Murna Ga Shugaba Biden

Bayan Shekara 245 da Samun Yanci, Shugaba Buhari Ya Aike da Saƙon Murna Ga Shugaba Biden

  • Shugaba Buhari ya taya takwaransa na ƙasar Amurka, Joe Biden, murnar ranar samun yancin kai
  • Buhari ya bayyana cewa ƙasashen Najeriya da Amurka sun haɗu a ɓangarori da dama kamar Demokaraɗiyya
  • Ya kuma ƙara da cewa za'a cigaba da ƙarfafa dangantakar ƙasashen biyu domin amfanar juna

Shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya aike da saƙon murna ga shugaban ƙasar Amurka, Joe Biden, yayin da ƙasarsa ke murnar cika shekaru 245 da samun yancin kai ranar 4 ga watan Yuli.

KARANTA ANAN: Kada Ku Sassauta Har Sai Kun Yi Kaca-Kaca da Yan Ta'addan Najeriya Baki Ɗaya, COAS Ga Sojoji

A wani rubutu da kakakin shugaban, Malam Garba Shehu, ya yi a shafinsa na dandalin sada zumunta facebook, Buhari ya taya Biden, Gwamnatin ƙasar, da al'ummar Amurka a dai-dai lokacin da suke murnar rana mai muhimmanci.

A saƙon shugaba Buhari, ya bayyana yadda gwamnatin Amurka take aiki ba dare ba rana domin shawo kan manyan ƙalubalen da take fuskanta da suka haɗa da wariyar launin fata da annobar COVID19 da ta yi mummunan ɓarna.

Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari
Bayan Shekara 245 da Samun Yanci, Shugaba Buhari Ya Aike da Saƙon Murna Ga Shugaba Biden Hoto: @MuhammaduBuhari
Asali: Instagram

Kyakkyawar Dangantakar mu zata cigaba da ƙarfafa

Buhari, a cikin saƙon da ya aike wa Biden, yace: "Muna kallo cikin shauƙi yadda gwamnatin Biden take samun cigaba a ƙoƙarin ta na kyautata alaƙarta da ƙawayenta na Africa da aiki tare domin kyautata ƙasashen."

"Ko dan saboda haɗuwar mu a demokaraɗiyya, dokoki, alaƙar Najeriya da Amurka zata cigaba da ƙarfafa."

KARANTA ANAN: JAMB Ta Tabbatar da Ɗalibai Sun Yi Mummunar Faɗuwa Bana, Ta Faɗi Dalili

Buhari ya kara da cewa za'a cigaba da ƙarfafa alaƙar dake tsakanin Najeriya da Amurka domin amfanin ƙasashen biyu.

Legit.ng hausa ta tattaro muku ra'ayoyin yan Najeriya a kan wannan labarin

Auwal Said Iyatawa, yace:

"Shugaba Biden da Shugaba Buhari sun haɗu wajen zuciyar yin aiki don kawo cigaba ga ƙasashen su, Allah ya ƙara taimakonsu."

Mairo Ado, tace:

"Shugaba Buhari Allah ya maka jagora da taimako a lamuranka, ya iya maka abinda zaka iya da wanda ba zaka iya ba."

Salihu Aspita Zainab, tace:

"Muna fatan Buhari ya ga adadin ayyukan yi da Amurka ta samar a ƙasar ta."

A wani labarin kuma Hoton Gwamna Zulum Yana Huɗa a Gonarsa, Ya Kai Ziyara Sansanin Yan Gudun Hijira

Gwamnan Borno, Farfesa Zulum yakai ziyara ɗaya daga cikin sansanin yan gudun hijira dake jiharsa.

Gwamnan yace mutanen dake rayuwa a irin waɗannan wurare abun tausayi ne matuƙa saboda ƙaruwar matsalar tsaro.

Asali: Legit.ng

Online view pixel