JAMB Ta Tabbatar da Ɗalibai Sun Yi Mummunar Faɗuwa Bana, Ta Faɗi Dalili

JAMB Ta Tabbatar da Ɗalibai Sun Yi Mummunar Faɗuwa Bana, Ta Faɗi Dalili

  • Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire JAMB ta amince ɗalibai sun faɗi jarabawar UTME 2021
  • Shugaban JAMB, Ishaq Oloyede, shine ya bayyana haka a wani shiri da ya halarta a gidan talabijin na ƙasa NTA
  • Yace yanayin yadda aka gudanar da karatu bana saboda annobar COVID19 da kuma matsalar tsaro sun taka rawa

Hukumar JAMB ta tabbatar da cewa ɗalibai sun faɗi jarabawar share fagen shiga makarantun gaba da sakandire UTME 2021 idan aka kwatanta da shekarun da suka gabata, kamar yadda premium times ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Gwarazan Yan Sanda Sun Yi Ruwan Wuta Kan Wasu Yan Bindiga da Suka Kai Hari Caji Ofis

Shugaban JAMB, Ishaq Oloyede, shine ya faɗi haka ranar Asabar yayin da ya bayyana a wani shirin talabijin na NTA, kamar yadda punch ta ruwaito.

Mr. Oloyede, ya ɗora alhakin wannan faɗuwar kan yadda aka gudanar da karatu a makarantu biyo bayan ɓarkewar annobar COVID19 da kuma ƙaruwar matsalolin tsaro a faɗin ƙasa.

JAMB Ta Tabbatar da Ɗalibai Sun Yi Mummunar Faɗuwa Bana
JAMB Ta Tabbatar da Ɗalibai Sun Yi Mummunar Faɗuwa Bana, Ta Faɗi Dalili Hoto: bbc.com
Asali: UGC

Shugaban ya musanta zargin cewa rashin cin jarabawar ɗalibai a bana zai shafi damar su ta samun gurbin karatu a manyan makarantu.

Ƙididdigar sakamakon ɗaliban da suka rubuta UTME

Da yake bayani kan ƙididdigar ɗaliban da suka rubuta jarawar, Mr. Oloyede ya bayyana cewa idan aka kwatanta sakamakon ɗalibai 400 da suka ci maki 120 zuwa sama a 2021 da 2020, akwai banbancin kashi 0.25%.

Yace amma abun yayi muni sosai idan aka kwatanta da sakamakon 2018 da 2019.

A cewar shugaban JAMB, a cikin ɗalibai 400 da duka rubuta jarabawar 2021, kashi 99.65 ne suka samu maki 120 zuwa sama amma a shekarar da ta gabata an samu kashi 99.80%.

Yace: "A 2018 mun samu kashi 99.99% amma a shekara mai biye mata 2019 sai ya sauka zuwa kashi 99.92%."

"A shekarar 2020, kashi 65.82 na ɗaliban da suka rubuta jarabawar sun samu maki 160 zuwa sama, amma a 2021 sai ya sauka zuwa kashi 65.62."

KARANTA ANAN: Hoton Gwamna Zulum Yana Huɗa a Gonarsa, Ya Kai Ziyara Sansanin Yan Gudun Hijira

Mr. Oloyede yace a shekarar 2019, daliban da suka ci maki sama da 300 daga cikin duk ɗalibai 400 ya kasance kashi 0.16%, yayin da ya ƙaru zuwa.0.26% a shekarar 2020, sannan ya sauka zuwa 0.06 a 2021.

A wani labarin kuma Ba Zan Taɓa Mantawa da Fasto Tunde Bakare ba, El-Rufa'i Ya Faɗi Alƙarsa da Faston Coci

Gwamna El-Rufa'i na jihar Kaduna ya bayyana kyakkyawar alaƙar dake tsakaninsa da Fasto Tunde Bakare, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

Gwamnan yace Fasto Bakare, shine ya gabatar da shi ga shugaban ƙasa Buhari da jam'iyyar CPC a baya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel