Hoton Gwamna Zulum Yana Huɗa a Gonarsa, Ya Kai Ziyara Sansanin Yan Gudun Hijira
- Gwamnan Borno, Farfesa Zulum yakai ziyara ɗaya daga cikin sansanin yan gudun hijira dake jiharsa
- Gwamnan yace mutanen dake rayuwa a irin waɗannan wurare abun tausayi ne matuƙa saboda ƙaruwar matsalar tsaro
- Gwamnan ya kuma kai ziyara gonarsa, inda aka hangeshi yana huɗa da kansa
Gwamnan Borno, Babagana Umaru Zulum, ya bayyana cewa yan gudun hijira na rayuwa cikin zullumi da baƙin ciki saboda ƙaruwar ayyukan ta'addanci, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.
KARANTA ANAN: Ba Zan Taɓa Mantawa da Fasto Tunde Bakare ba, El-Rufa'i Ya Faɗi Alƙarsa da Faston Coci
Gwamnan ya faɗi haka ne yayin da yakai ziyara sansanin yan gudun hijira dake Gubio.
Gwamnam ya kai ziyara sansanin ne domin duba aikin tantance yan gudun hijiran da kuma maida wasu daga ciki gidajensu dake ƙananan hukumomi 5.
Kananan hukumomin da mutanen suka fito sun haɗa da, Kukawa, Marte, Bama, Gwoza da kuma Ngala.
Mafi yawancin mutanen dake wannan sansanin na yan gudun hijira sun shafe kimanin shekaru 7 suna rayuwa a wurin.
Yayin ziyarar, Gwamnan Zulum yace duk waɗanda ke buƙatar komawa ƙauyukansu za'a maida su ba da jimawa ba, sannan kuma waɗanda aka samu zaman lafiya a yankin su za'a maida su gidajensu.
"Sauran yan gudun hijiran zamu sama musu wurin zama a yankunan dake da tsaro domin su cigaba da rayuwarsu kamar yadda suke a baya." inji Zulum.
KARANTA ANAN: Da Ɗuminsa: Bayan Komawarsa APC, Gwamna Matawalle Ya Sallami Dukkan Mashawartansa Na Musamman
Gwamna Zulum ya kai ziyara gonarsa
Bayan wannan ziyara ne, Zulum ya koma Dalwa, wani yankin dake da ƙasar noma mai kyau.
Gwamna Zulum da kansa ya yi huɗa a gonarsa, wacce yake kaiwa ziyara lokaci zuwa lokaci.
A wani labarin kuma Ministan Buhari Ya Ɓalle Daga Jam'iyyar APC, Ya Buɗe Sabuwar Sakateriya a Jiharsa
Jam'iyyar APC a jihar Kwara ta dare gida biyu, inda ministan yaɗa labaru, Lai Muhammed ya buɗe sabuwar sakateriya, kamar yadda punch ta ruwaito.
Rikicin cikin gida a jam'iyya mai mulkin Kwara ya fara ne tun bayan zargin da gwamna yayi wa wasu jiga-jigan jihar.
Asali: Legit.ng