An yi jana'izar tauraruwan Kannywood Zainab Booth a Kano

An yi jana'izar tauraruwan Kannywood Zainab Booth a Kano

  • A jiya Alhamis ne Allah ya yi wa jarumar Kannywood, Zainab Booth, rasuwa
  • Zainab Booth ta rasu tana da shekaru 61 a duniya bayan fama da gajeruwar rashin lafiya
  • An yi jana'izar ta a Kano inda daruruwan mutane suka hallarta ciki har da Ali Nuhu, Falalu Dorayi da Yakubu Mohammed

A yau Juma'a 2 ga watan Yuli ne aka yi jana'izar tauraruwan wasan kwaikwayo na hausa, Zainab Booth, wacce ta rasu a ranar Alhamis.

Premium Times ta ruwaito cewa a birnin Kano aka birne marigayiyar wacce ta rasu tana da shekaru 61 a duniya.

An yi jana'izar tauraruwan Kannywood Zainab Booth a Kano
An yi jana'izar tauraruwan Kannywood Zainab Booth a Kano. Hoto: Premium Times NG
Asali: Facebook

DUBA WANNAN: Hotunan Bindigu, Guraye, Layu da sauran kayan tsibbu da DSS ta samu a gidan Igboho yayin nemansa ruwa a jallo

Daruruwan abokan aikinta da masu aiki a masana'antar fim, irin su Ali Nuhu, Falulu Dorayi da Yakubu Mohammed da masoya da dama sun hallarci jana'izar.

Marigayiyar ta rasu ne bayan fama da gajeruwar rashin lafiya.

Domin tunawa da marigayiyar jarumar, jaruman Kannywood maza da mata da dama sun wallafa hotunanta a shafukansu na sada zumunta.

Dan uwanta, Ramadan Booth, shima ya yi addu'ar Allah ya jikarta da rahama ya gafarta mata.

Marigayiya Booth ta rasu ta bar yara hudu; biyu maza da biyu mata. Daya daga cikin yayanta mata ita ce fitaciyyar jaruma Maryam Booth.

KU KARANTA: 'Dan Majalisar PDP ya bayyana halin da Gwamnan Zamfara Bello Matawalle zai tsinci kansa a 2023

Abin da Maryam Booth ta ce game da mahaifiyarta Zainab Booth

A wani hirar da Premium Times ya yi da ita a 2020, Maryam ta ce mahaifiyarta ne abin alfaharinta a masana'antar na fim.

Maryam ta ce:

"Na girma na ga mahaifiya ta tana fitowa a fim kuma nima a hankali na bi sahunta."

Maryam ce tauraruwa a fina-finai kamar 'Gani Ga Ka' sannan ta fito a fim din 'Sons of the Caliphate.'

Zainab Booth ta yi fice a masana'antar fina-finan hausa saboda yawan fitowa a matsayin mahaifiya. Wasu daga cikin fina-finan da ta fito sune Mazan fama, Albashi, Rabuwa da Jarumai.

Asali: Legit.ng

Online view pixel