Jaruma Nafisa Abdullahi ta caccaki masu sukarta kan batun haifar yaran da ba a iya kula da su
- Jaruma Nafisat Abdullahi ta yi martani ga masu zaginta kan batun haihuwar yaran da ba a iya kula da su ko ake tura su almajiranci
- Jarumar tace ta san ance a yi aure a hayayyafa, amma babu inda aka ce a haifa a watsar da su a titi babu kulawa
- Ta ce ga masu cewa ta bari tayi aure kafin ta saka baki a wannan harkar, ta ina wannan ya shafi aurenta? Ko cewa tayi ba za ta taba aure ba babu abinda za a iya a kai
A kan batun jaruma Nafisat Abdullahi kuwa, jama'a sun yi caa a kanta bayan ta caccaki iyaye masu haifar 'ya'yan da basu iya kula da su ko suke tura su almajiranci.
Jarumar da alamu abun ya yi mata zafi inda ta zage tare da mayar musu da martani bayan ganin abun ya yi yawa yadda ake ta batun ta a kafafen sada zumunta har da jaridu.
A rubutu da tayi a shafinta na Twitter mai suna @NafisatOfficial, ta ce:
"Ya bayyana cewa wasu mutanen ba su ji dadin maganar da nayi ba, na cewa a daina haihuwar 'ya'yan da ba za a iya daukar nauyinsu ba. Eh, na san an ce ku yi aure ku hayayyafa, amma a ina aka ce ku haifa 'ya'yan ku watsar da su?
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Kun cika son bada kariya ga abunda kuka san cewa ba daidai bane. Suna cewa wai in bari in yi aure kafin in tsoma bakina a cikin irin wannan maganar. Toh ta ina rashin aurena ya shafi wannan maganar?"
Jarumar ta cigaba da cewa: "A yau idan nace ba zan yi aure ba, babu wanda ya isa yayi wani abu a kan hakan. Ma'ana ra'ayinku a kan aure na ba shi da wani amfani."
Ta kara da cewa: "Duk wanda yaji haushin nace a daina haihuwar 'ya'yan da ba za a iya daukar nauyinsu ba, Toh ya tabbata yana daga cikin matsalolin da muke fuskanta a arewa ko a kasar baki daya.
"Sannan a kalla abinda zai iya kawai shi ne ya yi zagi ko yace je ki yi aure, shikenan! Allah ya kyauta."
Batun lalata da matan fim: Nafisa Abdullahi ta saki martani ga Sarkin waka
A wani labari na daban, kamar yadda Legit.ng ta gano, batun da yafi yi wa 'yan Kannywood zafi a maganar sarkin waka shi ne batun lalata da mata kafin a saka su a fim inda matan Kannywood ke ta fitowa suna musanta waccan maganar da yayi.
Jaruma Nafisa Abdullahi ta rubuta budaddiyar wasika cikin harshen turanci a shafinta na Instagram kuma ta kara da bayani a kasan wasikar da harshen Hausa inda ta bayyana cewa babban zargi ya fitar tunda ta na cikin matan masana'antar.
Jarumar ta yi kira ga sarkin wakan idan ya na da matsala da wani ne, ya bayyana sunansa su yi ta kare ba wai ya bata masana'antar ba baki daya.
Asali: Legit.ng