Buhari ya nuna bakin cikinsa yayin da yake alhinin mutuwar dan majalisar Zamfara da wasu 'yan fashi suka kashe

Buhari ya nuna bakin cikinsa yayin da yake alhinin mutuwar dan majalisar Zamfara da wasu 'yan fashi suka kashe

  • Shugaba Buhari ya roki Allah da ya sanya wa dangin da ke jimamin rashin Muhammad Ahmad, dan majalisar dokokin jihar Zamfara dangana
  • A sakon ta’aziyyarsa, shugaban ya nuna alhininsa kan mutuwar Ahmad wanda wasu ‘yan bindiga suka kashe yayin da yake tuki zuwa Kano
  • Har zuwa rasuwarsa, Ahmad ya kasance dan majalisa mai wakiltar Mazabar Shinkafi a majalisar dokokin jihar ta Zamfara

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jajantawa dangin Muhammad Ahmad, dan majalisar jihar Zamfara da yan bindiga suka kashe kwanan nan akan hanyar Shema-Funtua, jihar Katsina, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

An harbe Ahmad ne yayin da yake tuka dansa zuwa Kano don hawa jirgi a daren Talata, 29 ga watan Yuni, bayan halartar taron gangamin maraba da Gwamna Bello Matawalle na Zamfara da ‘yan Majalisar Dokokin jihar zuwa Jam’iyyar APC.

KU KARANTA KUMA: Allah ya yi wa tsohuwar jarumar Kannywood, Zainab Booth rasuwa

Buhari ya nuna bakin cikinsa yayin da yake alhinin mutuwar dan majalisar Zamfara da wasu 'yan fashi suka kashe
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi alhinin mutuwar dan majalisar Zamfara Hoto: Femi Adesina
Asali: Facebook

An tattaro cewa yan bindigan sun kuma yi awon gaba da yaron dan majalisar da kuma direbansa.

Shugaba Buhari, a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Garba Shehu ya saki a ranar Alhamis, 1 ga watan Yuli, ya nuna alhinin rasuwar dan siyasar, kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito.

Shugaban kasar ya roki Allah Ya ji kan marigayin Ya sa ya huta. Ya kuma yi addu'ar Allah ya ba duk wadanda ke alhinin mutuwar mamacin juriya na wannan babban rashi.

KU KARANTA KUMA: Jagorancin APC a Zamfara: Yariman Bakura Ya Magantu Kan Cancantar Gwamna Matawalle

Shugaban na Najeriya ya ci gaba da nanata umarnin da ya ba hukumomin tsaro na yin maganin miyagu da ke son cutar da 'yan kasa da basu ji ba basu gani ba.

Matawalle Ya Yi Magana Kan Kisan Ɗan Majalisar Jiharsa, Ya Bayyana Alhininsa

A baya mun ji cewa Gwamna Matawalle na jihar Zamfara, ya nuna kaɗuwarsa kan kisan ɗan majalisar dokokin jihar mai wakiltar Shinkafi, Alhaji Muhammed G. Ahmed, wanda yan bindiga suka kashe ranar Talata da daddare, kamar yadda leadership ta ruwaito.

A wani jawabi da kakakin gwamnan, Yusuf Idris Gusau, ya fitar, gwamnan ya bayyana marigayin a matsayin mutumin kirki kuma mai juriya.

Matawalle yace yaji labari mara daɗi na mutuwarsa kuma ya kaɗu matuƙa saboda marigayin yana tare da shi kwana ɗaya kafin faruwar lamarin yayin sauya shekarsa zuwa APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel