Matawalle Ya Yi Magana Kan Kisan Ɗan Majalisar Jiharsa, Ya Bayyana Alhininsa

Matawalle Ya Yi Magana Kan Kisan Ɗan Majalisar Jiharsa, Ya Bayyana Alhininsa

  • Gwamnan Zamfara, Bello Matawalli, ya yi jimamin kisan da aka yiwa ɗan majalisar dokokin jiharsa, Hon. G. Ahmed
  • Gwamnan yayi ta'aziyya ga iyalan mamacin tare da addu'ar neman samun rahamar ubangiji
  • Gwamnan ya samu halartar sallar jana'iza da aka yi wa marigayi Ahmed a masallacin Sheikh Umar Kanoma

Gwamna Matawalle na jihar Zamfara, ya nuna kaɗuwarsa kan kisan ɗan majalisar dokokin jihar mai wakiltar Shinkafi, Alhaji Muhammed G. Ahmed, wanda yan bindiga suka kashe ranar Talata da daddare, kamar yadda leadership ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Ba Zamu Huta ba Har Sai Mun Tabbatar da Yan Najeriya Na Bacci da Ido Biyu, IGP

A wani jawabi da kakakin gwamnan, Yusuf Idris Gusau, ya fitar, gwamnan ya bayyana marigayin a matsayin mutumin kirki kuma mai juriya.

Gwamna Matawalle yayi jimamin kashe ɗan majalisa
Matawalle Ya Yi Magana Kan Kisan Ɗan Majalisar Jiharsa, Ya Bayyana Alhaninsa Hoto: leadership.ng
Asali: UGC

Matawalle yace yaji labari mara daɗi na mutuwarsa kuma ya kaɗu matuƙa saboda marigayin yana tare da shi kwana ɗaya kafin faruwar lamarin yayin sauya shekarsa zuwa APC.

"Ɗan majalisar ya bada gudummuwarsa sosai wajen ganin an gudanar da taron sauya shekar mu, ba tare da sanin wannan shine aikinsa na ƙarshe ba," inji gwmnan.

Matawalle yayi addu'ar samun rahama da mamacin

Gwamnan ya yi addu'ar Allah ya gafaratawa marigayi Ahmed, yasa aljanna ce makomarsa, sannan yayi addu'a Allah ya baiwa iyalansa juriyar wannan rashi da suka yi.

KARANTA ANAN: Mun San Inda Yan Bindiga Suka Ɓoye Ɗaliban Islamiyyar Tegina, Gwamnatin Neja

Matawalle ya halarci sallar jana'iza da aka yi wa mamacin tare da ɗaruruwan mutane wanda ya gudana a masallacin jumu'a na Sheikh Umar Kanoma.

A wani labarin kuma Yan Majalisa Sun Bankaɗo Wata Sabuwar Badaƙala a Rundunar Sojin Ƙasa, Zasu Fara Bincike

Majalisar wakilai ta gano wata badaƙala a rundunar sojin ƙasa ta rashin biyan ƙananan sojoji alawus ɗinsu, kamar yadda channels tv ta ruwaito.

Majalisar ta umarci kwamitin ta dake kula al'amuran sojojim ƙasa ya gudanar da bincike kan lamarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262