‘Yan adaidaita sahu a Kano za su biya N100,000 don samun sabon lasisin tuki - Hukumar KAROTA

‘Yan adaidaita sahu a Kano za su biya N100,000 don samun sabon lasisin tuki - Hukumar KAROTA

  • Hukumar KAROTA ta ce daga yanzu masu bukatar lasisin tuka adaidaita sahu N100,000 za su biya sabanin N8,000 na baya
  • Shugaban Hukumar, Baffa Babba Dan Agundi ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da ya fitar yayin ganawa da manema labarai ranar Laraba
  • A cewarsa, Gwamnatin Jihar ta bayar da isasshen lokaci amma wasu masu kunnen kashi suka kekashe suka ki yi a kan lokacin da aka bayar

Hukumar kula da hanyoyi da ababen hawa ta jihar Kano (KAROTA) ta ce ‘yan adaidaita sahu da ke bukatar samun sabon lasisin tuki a jihar dole ne su biya kudi N100,000 kafin su sami lasisin tuki.

Tashin kudin daga N8,000 na baya ya kasance ne sakamakon karewar wa'adin da aka baiwa matukan tun farko, a cewar hukumar.

KU KARANTA KUMA: Da duminsa: Kotu ta tsare shahararren jigon APC a gidan kurkuku

‘Yan adaidaita sahu a Kano za su biya N100,000 don samun sabon lasisin tuki
A baya N8000 ake biya domin mallakar lasisin tukin adaidaitar Hoto: Aminiya
Asali: UGC

Manajan daraktan hukumar, Baffa Babba Dan-Agundi ne ya bayyana hakan a ranar Laraba yayin ganawa da manema labarai a Kano, jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban ya ce:

“Ga duk wanda ya ki yin rajista a da, yanzu dole ne ya biya N100,000.
“A da, lasisin tukin ya kasance N8,000, yanzu zai zama N100,000 saboda za ka ga shigowar sabbin mutane a jihar Kano.
“Dole ne mu dauki matakan magance wannan. Ba ku yi rajista ba a lokacin da muka ba da dama, yanzu za ku biya N100,000 don samun izinin yin aiki.”

Ya bayyana cewa aiwatar da sabon umarnin zai fara nan take kuma wadanda aka kama za a gurfanar da su a kotu.

KU KARANTA KUMA: Da Duminsa: Wasu Daga Cikin Daliban Islamiyya da Aka Sace a Jihar Neja Sun Tsere

Baffa Babba ya ce a yanzu akwai baburan Adaidaita Sahu 60,0000 masu lasisi da ake harkokin sufuri da su a Jihar Kano.

Kan batun karbar haraji, Dan Agundi ya ce Hukumar Tattara Haraji ta Jihar Kano KIRS ce ke da alhakin karba a yayin da nauyin da rataya a kan tasu hukumar ya takaita kadai a kan aiwatarwa, jaridar Aminiya ta ruwaito.

Direbobin keke napep sun dage yajin aiki a jihar Kano

A wani labarin, a baya mun ji cewa direbobin keke napep dake yajin aiki a Kano sun dakatar da matakin kuma za su ci gaba da aiki ba tare da bata lokaci ba.

Shuwagabanin hadin kan kungiyoyin masu keke napep na Najeriya sun umarci membobinsu da su ci gaba da aiki nan take.

Shugaban kungiyar, Mansur Tanimu ne ya tabbatar da haka a ranar Talata a tattaunawarsa da Aminiya ta wayar tarho.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng