Kashi 90 na ‘yan aji biyar sun fadi jarrabawar kwalifai a Jihar Kano

Kashi 90 na ‘yan aji biyar sun fadi jarrabawar kwalifai a Jihar Kano

  • Lamari irin wannan kan kara samar da daliban da ke barin zuwa makaranta
  • Iyaye da dama ba za su iya yi wa ‘ya’yansu rajistar ba
  • Wani malamin ya ce cikin 300 da suka zana jarrabawar kwalifai din guda 6 ne kacal suka ci jarrabawar

Kimanin kashi 90 na daliban da suka rubuta jarrabawar kwalifai a Jihar Kano sun gaza tabuka wani kwazo.

Cin jarrabawar ta kwalifai kan bai wa dalibi damar gwamnatin jihar ta biya masa kudin rubuta babbar jarrabawar kammala sakandare.

Har sai dalibi ya samu sakamako mai kyau wato kiredit a darussa bakwai ciki har da darasin Lissafi da na Turancin Ingilishi.

Sai dai sakamakon jarrabawar da aka fitar kwana uku da suka gabata, kafin karewar wa’adin rajistar jarrabawar NECO, ya nuna daliban sun fadi warwas.

Kashi 90 na ‘yan aji biyar sun fadi jarrabawar kwalifai a Jihar Kano
Kashi 90 na ‘yan aji biyar sun fadi jarrabawar kwalifai a Jihar Kano
Asali: Twitter

A wani rahoton jaridar Daily Trust ta ce wa’adin rufe rajistar jarrabawar NECO ya yi matukar kadan ga daliban da suka fadi jarrabawar kwalifai din su iya samun kudin rajistar jarrabawar ta NECO.

Kudin rajistar NECO ya kai N12, 000 zuwa N13, 000.

A fadin wani malamin wata makaranta a jihar ya ce cikin dalibai fiye da 300 da suka zana jarrabawar, shida ne kacal suka samu sakamako mai kyau.

Malamin ya ce hakan zai sanya da dama daga cikinsu ko dai su maimata ajin ko kuma su bar karatun gaba daya.

Yace:

“Galibi irin wadannan matsalolin ne ke sanyaya gwiwar dalibai su dakatar da karatun.
“Galibin wadanda suka fadi jarrabawar ba su da kudin da za su yi rajistar jarrabawar ta NECO.
“Kuma maimakon su maimaita ajin sai kawai su watsar da karatun dungurumgum saboda ba su da tabbas me zai faru a badin.
“Irin abin da ke taimaka wa wajen karuwar yawan yaran da suka bar karatun boko a yankin nan.”

Wani malamin kuma cewa ya yi dalibai 60 ne cikin 200 suka ci jarrabawar kwalifai a makarantar da yake koyarwa. Sannan ya ce daliban da suka biya kudin jarrabawar ta NECO ba su haura 40 cikin 140 din da suka fadi jarrabawar kwalifai.

A cewarsa, gwamnatin ta fitar da sakamakon jarrabawar ta kwalifai a makare sosai. Ya kara da cewa akasarin iyaye ba za su iya hada kudin rajistar NECO ba cikin kwana uku ko hudu.

Wani dalibi mai suna, Usama Sa’adu, ya ce tuni har ya fitar da ran zana jarrabawar NECO a bana saboda ba shi da kudin rajista.

“Babana ba zai iya biya mini kudin rajistar ba maganar gaskiya, ni kuma ba ni da ikon in biya wa kaina.

“Don haka a yanzu dai ban san ma mene ne zan yi a kai. Abin da na sani kawai shi ne idan ban zana jarrabawar NECO ba to ba zan sake koma wa makaranta ba domin ban san ko zan samu nasara a badi, " inji shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng