Wani Jigon Jam'iyyar PDP Ya Buƙaci INEC Ta Dakatar da Sauya Sheƙar Gwamnoni Zuwa APC
- Jigon PDP a jihar Kwara, Alhaji Abdulƙadir Oba Ajara, ya yi kira ga INEC ta duba sauya sheƙar gwamnoni
- Ajara ya buƙaci INEC ta yi amfani da kundin dokokin zaɓe na ƙasa ta ɗauki mataki a kan waɗannan gwamnonin
- Ya kuma yi kira ga yan Najeriya waɗanda suka isa kaɗa kuri'a da su fito su yi rijistar zaɓe
Wani jigo a babbar jam'iyyar hamayya PDP ta jihar Kwara, Alhaji Abdulƙadir Oba Ajara, yayi kira ga hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) da ta duba wannan yawaitar sauya sheƙar gwamnoni daga wata jam'iyya zuwa wata, kamar yadda leadership ta ruwaito.
KARANTA ANAN: Shugaba Buhari Ya Taya Matawalle Murna, Ya Faɗi Dalilin Gwamnan Na Sauya Sheƙa Zuwa APC
Ajara, wanda yayi jawabi ga manema labarai ranar Talata a Ilorin, yace wannan bikin sauya sheƙar ba zai haifar da ɗa mai ido a cigaban demokaradiyyar ƙasar nan ba.
Ya ƙara da cewa duk yanayin da za'a ce gwamna zai canza jam'iyya kuma mataimakinsa na wata jam'iyya ta daban ba yanayi ne mai kyau ba.
Ajara yace matuƙar gwamna da mataimakinsa zasu kasance a jam'iyya daban-daban to ba za'a samu jagoranci mai kyau ba.
Yace: "Ina kira ga hukumar zaɓe INEC da ta yi amfani da dokokin zaɓen ƙasar nan a kan gwamnonin dake sauya sheƙa, ta ɗauki matakin da ya dace."
KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Dalilin da Yasa Na Gudu, Nnamdi Kanu Yayi Jawabi a Gaban Kotu
Jigon PDP yayi kira ga INEC ta tsaftace aikin rijistar zaɓe
Hakanan kuma, Ajara, ya yi kira ga hukumar zaɓe da ta tabbatar da aikin rijistar zaɓe da aka cigaba ya tafi yadda ya kamata.
Hakazalika yayi kira ga yan Najeriya waɗanda shekarunsu suka kai na yin zaɓe da su fito ƙwanso da ƙwarkwatarsu su yi rijistar zaɓe.
A wani labarin kuma Jigon PDP Ya Caccaki El-Rufa'i, Ya Buƙaci Ya Sadaukar da Albashinsa Ga Ɗalibai
Jigon jam'iyyar PDP, Lawal Adamu Usman, ya ƙalubalanci gwamnan Kaduna kan ɗaukar nauyin ɗalibai, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.
Adamu yace akwai ɗalibai da dama da ba zasu iya biyan kuɗin makarantar su ba saboda ƙarin da gwamnati ta yi.
Asali: Legit.ng