Da Ɗumi-Ɗumi: Dalilin da Yasa Na Gudu, Nnamdi Kanu Yayi Jawabi a Gaban Kotu
- Shugaban ƙungiyar tawaren IPOB da aka kama ya yi magana a gaban kotu, ya faɗi dalilin da yasa ya fice daga Najeriya
- A shekarar 2017 alkalin babbar kotun tarayya dake Abuja, Binta Nyako, ta bada belin Kanu bisa sharuɗɗa masu tsauri
- Amma duk da haka sai da Kanu ya tsallake dukan sharuɗɗan ya fice Najeriya
Shugaban ƙungiyar yan taware IPOB, Nnamdi Kanu, ya bayyana dalilin da yasa ya fice daga Najeriya bayan an bada belinshi a shekarar 2017, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.
Yace ya ɗauki matakin guduwa ne saboda an zagaye gidansa amma duk da haka saida ya samu nasarar ficewa, kamar yadda premium times ta ruwaito.
KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Wani Gwamna Ya Kori Ma'aikata da Dama a Jiharsa, Ya Tilasta Wa Wasu Yin Ritaya
Kanu ya ƙara da cewa idan bai tsere ba, to za'a iya kashe shi kamar yadda ake yiwa sauran mambobin ƙungiyar IPOB.
Binta Nyako ta bada belin Kanu a 2017
Alƙalin babbar kotun tarayya dake Abuja, Binta Nyako, itace ta bada belin Kanu bisa wasu dalilai na rashin lafiya a shekarar 2017.
Alƙalin ta gargaɗi wanda ake ƙara da kada ya kuskura a ganshi a cikin taron mutum 10 ko kuma a ganshi a cikin wani gangamin taro.
Amma duk da haka, Kanu ya tsallake waɗannan sharuɗɗan belin nasa, ya fice daga Najeriya, kuma daga can ya dinga umartan mambobin ƙungiyarsa.
KARANTA ANAN: Da Ɗuminsa: FG Ta Faɗi Ranar da Zata Kulle Layukan Wayar da Ba'a Haɗasu da NIN Ba
An Buƙaci kotu ta riƙe Kanu a ofishin DSS
A ranar Talata, mai baiwa Antoni Janar Shawara, Shuaibu Labaran, ya shaida wa kotu cewa an damƙe Nnamdi Kanu kuma aka gabatar da shi gaban Kotu.
Labaran ya roƙi kotun da ta bada umarnin a rufe shugaban IPOB ɗin da aka kama a hedkwatar hukumar tsaron DSS.
Yace: "Muna roƙon kotu da ta bada umarnin tsare shugaban IPOB da aka kama a ofishin DSS."
Alkali Nyako, ta ɗage sauraron ƙarar har sai ranar 26 ga watan Yuli za'a cigaba da gudanar da shari'ar.
A wani labarin kuma Wani Tsohon Kwamishina Ya Sha da Ƙyar Yayin da Yan Bindiga Suka Buɗe Wa Motocinsa Wuta
Tsohon kwamishina a jihar Ondo, Joseph Ikpea, ya sha da ƙyar a hannun masu garkuwa da mutane, kamar yadda punch ta ruwaito.
Rahoto ya bayyana cewa Ikpea yana cikin bacci wasu yan bindiga suka buɗe wa tawagar motocinsa wuta.
Asali: Legit.ng