Jigon PDP Ya Caccaki El-Rufa'i, Ya Buƙaci Ya Sadaukar da Albashinsa Ga Ɗalibai

Jigon PDP Ya Caccaki El-Rufa'i, Ya Buƙaci Ya Sadaukar da Albashinsa Ga Ɗalibai

  • Jigon jam'iyyar PDP, Lawal Adamu Usman, ya ƙalubalanci gwamnan Kaduna kan ɗaukar nauyin ɗalibai
  • Adamu yace akwai ɗalibai da dama da ba zasu iya biyan kuɗin makarantar su ba saboda ƙarin da gwamnati ta yi
  • Yayi kira ga gwamna El-Rufa'i na jihar Kaduna da ya sadaukar da albashinsa na wata-wata wajen baiwa ɗalibai tallafi

Wani jigon babbar jam'iyyar hamayya ta PDP, Lawal Adamu Usman, ya roki gwamnan Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa'i, ya sadauƙar da albashinsa wajen ɗaukar nauyin karatun ɗalibai, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Dalilin da Yasa Na Gudu, Nnamdi Kanu Yayi Jawabi a Gaban Kotu

Wannan kiran yazo ne bayan gwamnatin jihar Kaduna ta ƙara kuɗin makaranta ga ɗaliban dake karatu a makarantun gaba da sakandire mallakin jihar.

Malam Nasiru El-Rufa'i
Jigon PDP Ya Caccaki El-Rufa'i, Ya Buƙaci Ya Sadaukar da Albashinsa Ga Ɗalibai Hoto: arise.tv
Asali: UGC

Da yake jawabi a wurin bada tallafin karatu da gidauniyar Lawal Adamu Usman ta yi ga ɗalibai 100 a Kaduna, jigon PDP ya yi kira ga gwamnan Kaduna ya zama shugaba abin koyi, ya sadaukar da kuɗin albashinsa wajen biyawa ɗaliban Ƙaduna kuɗin makaranta.

A jawabinsa, yace: "Ba abinda zai ragi gwamnan idan ya zama adalin shugaba da za'a rinƙa bada misali da shi, ya sadaukar da albashinsa na wata-wata ga ɗalibai waɗanda ba su iya biyan kuɗin makarantarsu."

Gidauniyarsa ta bada tallafin miliyan N30 ga ɗaliban Kaduna

Lawal Adamu ya bayyana cewa gidauniyarsa ta bada tallafin karatu na kimanin miliyan N30m ga ɗalibai a jami'ar jihar Kaduna (KASU), Kwalejin fasaha ta Nuhu Bamalli, da kwalejin ilimi dake gidan waya.

Yace gidauniyar ta samu nasarar samar da tallafin karatu ga ɗalibai 100 daga cikin ɗalibai 10,000 da suka nemi tallafin.

KARANTA ANAN: Da Ɗumi-Ɗumi: Wani Gwamna Ya Kori Ma'aikata da Dama a Jiharsa, Ya Tilasta Wa Wasu Yin Ritaya

Yace: "Mun tallafawa ɗalibai da naira miliyan N30m, kuma muna sa ran ƙara kuɗin su kai miliyan N50m a shekara mai zuwa."

"Mun fara biyan kuɗin makarantar waɗanda suka amfana da tallafin na N107,000 ga tsaffin dalibai, da kuma naira N150,000 ga sabbin ɗalibai."

A wani labarin kuma Ba Gudu Ba Ja da Baya a Matakin Mu Na Korar Ma'aikata, El- Rufa'i Ya Faɗawa Buhari

Gwamnan Kaduna, El-Rufa'i, ya shaida wa shugaba Buhari sabon kudirin da gwamnatinsa ta bullo da shi na yin gyara

Gwamnan yace a halin yanzun an fara aikin ɗaukar ma'aikata 10,000 a jihar Kaduna, kamar yadda channels tv ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel