Jerin sunaye da hotunan gwamnonin APC da ke Zamfara a yanzu haka don sauyin shekar Matawalle

Jerin sunaye da hotunan gwamnonin APC da ke Zamfara a yanzu haka don sauyin shekar Matawalle

  • Manyan jiga-jigan jam'iyyar APC sun hallara a jihar Zamfara gabannin sauya shekar Gwamna Bello Matawalle
  • Daga cikin wadanda suka hallara akwai gwamnonin APC masu ci da kuma tsoffin gwamnonin jam'iyyar
  • Ana shirye-shiryen tarban gwamnan na Zamfara wanda zai sauya sheka daga PDP zuwa APC a hukumance a yau Talata, 29 ga watan Yuni

Gabanin sauya shekar da Gwamna Bello Matwalle ke shirin yi zuwa jam'iyyar All Progressives Congress (APC), masu ruwa da tsaki na jam'iyya mai mulki sun hallara a jihar Zamfara.

Taron ya samu halartar tsoffin gwamnonin jihar Zamfara biyu, Abdulaziz Yari da Mahmud Shinkafi, da tsoffin sanatoci, ministoci da shugaban APC na jihar, Lawal Liman.

KU KARANTA KUMA: Gwamnatin tarayya ta gurfanar da Mahdi kan zargin batanci ga Masari

Jerin sunaye da hotunan gwamnonin APC da ke Zamfara a yanzu haka don sauyin shekar Matawalle
Manyan jiga-jigan APC sun yi wa Zamfara tsinke gabannin sauya shekar Bello Matawalle Hoto: Buhari Sallau
Asali: Facebook

Hadimin Shugaban kasa Muhammadu Buhari a shafukan sadarwar zamani, Buhari Sallau ne ya wallafa hotunan a shafinsa na Facebook.

Ga jerin jiga-jigan APC da suka hallara

1. Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe kuma shugaban kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar APC mai rikon kwarya

2. Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi

3. Gwamna Abubakar Bagudu na jihar Kebbi

4. Gwamna Mohammed Badaru Abubakar na jihar Jigawa

5. Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno

6. Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna

7. Tsohon gwamna, Abdulaziz Yari, shugaban jam'iyyar APC a jihar Zamfara

8. Tsohon gwamna Ali Modu Sheriff na jihar Borno

KU KARANTA KUMA: Da dumi-dumi: PDP na cikin matsala yayinda Sanatan Zamfara ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar

Martanin jama’a kan taron

Nsidibe James ya yi martani cewa:

“Zai yi nadamar shawarar da ya yanke.”

Kalidu Idris ya ce:

“Ina taya ku murna.”

Justice Dogo ya ce:

“Ina maku fatan tattaunawa mai amfani, don ku fitar da dabaru masu kyau wadanda zasu gina Al'umma.”

Yahaya Nuhu Kaya ya ce:

“Ta tabbata dai Shehi ne chiaman Allah yasa albarka Allah yasa mu gyara kura kuranmu, Gaba dai APC ina son babbar jam’iyyata.”

APC Ta Shirya Babban Gangami Yayin da Jiga-Jiganta Zasu Dira Jihar Zamfara

A wani labarin, Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, zai tabbatar da komawarsa jam'iyyar APC a ranar Talata.

Saboda haka ne jam'iyyar ta shirya wani babban gangami na tarbar gwamna Matawalle zuwa APC wanda zai gudana a Trade Fair dake Gusau, babban birnin Zamfara da misalin ƙarfe 10 na safe, kamar yadda punch ta ruwaito.

Ana sa ran jiga-jigan jam'iyyar APC na ƙasa da na jihar Zamfara ne zasu karɓi gwamnan, kamar yadda the nation ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng