Gwamnatin tarayya ta gurfanar da Mahdi kan zargin batanci ga Masari
- Gwamnatin tarayya ta gurfanar da wani mai sukar gwamnatin jihar Katsina, Muhammad Mahdi
- An ce Mahdi ya zargi gwamnan jihar, Bello Masari, da yin almubazzaranci da naira biliyan 62 na baitulmalin Katsina
- A cewar rahoton, Mahdi ya kuma bayyana cewa Masari ya amince da N500bn don taron APC a Abuja, babban birnin kasar
Gwamnatin tarayya ta gurfanar da wani mai sukar lamura, Muhammad Mahdi, bisa zargin bata sunan gwamnan jihar Katsina, Aminu Bello Masari.
Jaridar The Punch ta ruwaito cewa Mahdi ya kuma bata sunan gwamnati da na Sakataren Gwamnatin jihar, Mustapha Inuwa.
KU KARANTA KUMA: Da dumi-dumi: PDP ta rasa mambobinta 2 a majalisar wakilai, sun sauya sheka zuwa APC
Legit.ng ta tattaro cewa an tsare Mahdi ne bisa zargin tunzura jama'a akan su ukun.
Mahdi, wanda aka gurfanar da shi a gaban wata Babbar Kotun Tarayya da ke zaune a Kano kan tuhume-tuhume shida da suka shafi cin zarafi, ya musanta aikata dukkan laifukan.
ACP Simon Lough, lauya mai shigar da kara, ya zargi Mahdi da karya ka’idojin belinsa da kuma buga sabbin labaran batanci 32 daga Maris 2021 zuwa 28 ga Yuni 2021, akan Masari a yanar gizo.
KU KARANTA KUMA: Da dumi-dumi: PDP na cikin matsala yayinda Sanatan Zamfara ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar
A cewar rahoton, an ce Mahdi ya zargi Masari da almubazzaranci da N62bn na baitulmalin Katsina, N64b na tsaro sannan kuma ya ce gwamnan ya amince da N500bn don taron jam’iyyar APC a Abuja.
Mai shari’a A. Lima, alkalin da ke jagorantar shari’ar, ya dage sauraron karar zuwa ranar 26 da 27 ga watan Yulin 2021 don ci gaba da sauraro.
Me Ya Rage Nake Nema: Masari Ya Ce Daga 2023 Zai Yi Sallama da Siyasa
A wani labarin, Gwamnan jihar Katsina, Aminu Masari, ya ce zai yi ritaya daga siyasa bayan kammala wa'adinsa na Gwamna.
Masari ya bayyana hakan ne yayin zantawarsa da manema labarai a wani bangare na shagalin bikin ranar dimokradiyya ta kasa a Katsina ranar Asabar.
Ya bayyana cewa zai yi ritaya zuwa gonarsa bayan ya kammala wa'adinsa na Gwamnan jihar, Daily Nigerian ta ruwaito.
Asali: Legit.ng