Hotunan gwamnoni, ministoci da jiga-jigan da suka je fadar Kano nemawa Yusuf Buhari aure

Hotunan gwamnoni, ministoci da jiga-jigan da suka je fadar Kano nemawa Yusuf Buhari aure

  • Jiga-jigai a kasar nan da suka hada da gwamnoni, ministoci da masu mukaman siyasa sun je nemawa Yusuf Buhari aure
  • Tawagar da ta sauka a fadar Aminu Ado Bayero ta samu shugabancin Gwamna Badaru tare da Sanata Ali Modu, Zulum da sauransu
  • An saka ranar bikin Yusuf Buhari da Zahra Bayero inda za a sha shagali a cikin watannin Augusta da Satumba

Manyan masu mukaman siyasa wadanda suka wakilci fadar shugaban kasa sun isa fadar sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero domin nemawa da daya tilo na shugaban kasa Muhammadu Buhari, Yusuf Buhari aure.

Gwamnan jihar Jigawa, Abubakar Badaru, ya jagoranci wakilan zuwa fadar a ranar Lahadi, 27 ga watan Yuni tare da wasu gwamnoni da manyan jami'an gwamnati da suka hada da ministan shari'a, Abubakar Malami, shafin Linda Ikeji ya ruwaito.

Hotunan gwamnoni, ministoci da jiga-jigan da suka je fadar Kano nemawa Yusuf Buhari aure
Hotunan gwamnoni, ministoci da jiga-jigan da suka je fadar Kano nemawa Yusuf Buhari aure. Hoto daga lindaikejisblog.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Zulum ya kori NGO mai suna ACTED bayan an kama su suna koyar da harbi a Maiduguri

An sanya ranar auren Yusuf da Zahra Bayero, diyar sarkin Bichi, Alhaji Dr. Nasir Bayero, mai shekaru 19 a jihar Kano.

Yusuf da Zahra Nasir sun hadu ne a jami'ar Surrey dake Ingila inda Zahra ke karanta fannin fasahar zanen gine-gine. Za a yi aure a cikin watannin Augusta da Satumban 2021.

Hotunan gwamnoni, ministoci da jiga-jigan da suka je fadar Kano nemawa Yusuf Buhari aure
Hotunan gwamnoni, ministoci da jiga-jigan da suka je fadar Kano nemawa Yusuf Buhari aure. Hoto daga lindaikejisblog.com
Asali: UGC

Sauran wadanda suka wakilci iyalan shugaban kasa Muhammadu Buharin sun hada da gwamnan jihar Borno, Umaru Zulum, Sanata A. Amosun, tsohon gwamnan jihar Zamfara, Abdulaziz Yari, shugaban jami'an tsaro na farin kaya, Yusuf Bichi, Farfesa Abdullahi Abba, Malam Ahmed, Sanata Ali Modu Sheriff, Sanata Tanko Almakura da sauransu.

Hotunan gwamnoni, ministoci da jiga-jigan da suka je fadar Kano nemawa Yusuf Buhari aure
Hotunan gwamnoni, ministoci da jiga-jigan da suka je fadar Kano nemawa Yusuf Buhari aure. Hoto daga lindaikejisblog.com
Asali: UGC

Mahaifiyar Zahra, Farida Imam, diya ce ga fitaccen malamin Kano, Malam Abubakar Imam wanda aka fi sani da Imamu Galadanci, tsohon daraktan Afribank Plc, Daily Trust ta ruwaito.

Hotunan gwamnoni, ministoci da jiga-jigan da suka je fadar Kano nemawa Yusuf Buhari aure
Hotunan gwamnoni, ministoci da jiga-jigan da suka je fadar Kano nemawa Yusuf Buhari aure. Hoto daga lindaikejisblog.com
Asali: UGC

KU KARANTA: Ganduje na kokarin tsige Rimingado saboda bincikar iyalansa da yake kan wasu kwangiloli

A wani labari na daban, duk da hadin kan da aka samu tsakanin bangarorin Boko haram da na ISWAP, ragargaza da luguden wutan da dakarun sojin saman Najeriya suka yi a yankin tafkin Chadi ya tarwatsa manyan sansanin 'yan ta'addan.

Kamar yadda Vanguard ta ruwaito, majiyoyi sun bayyana cewa harin da sojojin suka kai bayan bayanan sirrin da suka samu an yi shi ne domin tarwatsa sansanin 'yan ta'adda dake Sabon Tumbu, Jibularam da Kwalaram.

Wannan cigaban yana zuwa ne bayan wani rahoto da aka samu na hadin kan 'yan ta'addan Boko Haram da na ISWAP a wani bidiyo mai mintuna goma sha uku wanda ke nuna sun hada hannaye suna furta kalaman hadin kai, lamarin dake bayyana hadin kai da tarayya a tsakaninsu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel