Kwamandojin Boko Haram da ISWAP na taro, NAF sun yi luguden wuta a yankin tafkin Chadi

Kwamandojin Boko Haram da ISWAP na taro, NAF sun yi luguden wuta a yankin tafkin Chadi

  • Sojin saman Najeriya sun yi luguden wuta tare da ragargazar sansanin 'yan ta'adda dake tafkin Chadi
  • Akwai yuwuwar babban kwamanda Ali Chakkar da wasu jiga-jigai sun sheka lahira saboda ruwan wutar
  • NAF ta tabbatar da cewa ta kai harin a Sabon Tumbu, Jibularam da Kwalaram mai cike da nasarori

Duk da hadin kan da aka samu tsakanin bangarorin Boko haram da na ISWAP, ragargaza da luguden wutan da dakarun sojin saman Najeriya suka yi a yankin tafkin Chadi ya tarwatsa manyan sansanin 'yan ta'addan.

Kamar yadda Vanguard ta ruwaito, majiyoyi sun bayyana cewa harin da sojojin suka kai bayan bayanan sirrin da suka samu an yi shi ne domin tarwatsa sansanin 'yan ta'adda dake Sabon Tumbu, Jibularam da Kwalaram.

KU KARANTA: FG tana sane da alakata da 'yan bindiga, Sheikh Gumi ya yi bayani

Kwamandojin Boko Haram da ISWAP na taro, NAF sun yi luguden wuta a yankin tafkin Chadi
Kwamandojin Boko Haram da ISWAP na taro, NAF sun yi luguden wuta a yankin tafkin Chadi. Hoto daga @MobilePunch
Asali: UGC

KU KARANTA: Amurka: An yankewa dan sandan da ya kashe bakar fata Floyd shekaru 22.5 a gidan yari

Cikin kwanakin nan ISWAP da Boko Haram suka hade

Wannan cigaban yana zuwa ne bayan wani rahoto da aka samu na hadin kan 'yan ta'addan Boko Haram da na ISWAP a wani bidiyo mai mintuna goma sha uku wanda ke nuna sun hada hannaye suna furta kalaman hadin kai, lamarin dake bayyana hadin kai da tarayya a tsakaninsu.

Daily Nigerian ta ruwaito cewa, wata majiyar sirri wacce aka yi ragargazar da ita ta ce jirgin yakin sojin ya kone wurin bauta da horar da 'yan ta'adda a yankin arewa maso gabas a jihar Borno da kuma yankin tafkin Chadi.

Akwai yuwuwar Ali Chakkar da manyan kwamandoji sun mutu

"Bayanin sirri ya tabbatar da cewa Ali Chakkar da sauran manyan kwamandojin ISWAP na taro yayin da aka kaddamar da harin.

"Luguden wutan da sojojin saman suka yi kuwa ya janyo halakar 'yan ta'addan ISWAP da na Boko Haram masu tarin yawa."

NAF ta tabbatar da luguden wutan

Mai magana da yawun rundunar sojin saman Najeriya, Air Commodore Edward Gabkwet ya tabbatar da aukuwar harin a wuraren a yayin da PRNigeria ta tuntube shi.

Ya ce: "Bamu banbancewa tsakanin 'yan ta'addan Boko haram da na ISWAP amma mun kaddamar da hari mai cike da nasara ta jiragen yaki."

A wani labari na daban, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce jam'iyyar APC ta dawo kamar yadda take kuma ta tsallake dukkan matsalolin dake cikin jam'iyyar.

Shugaban kasar ya ce jam'iyyar ta farfado, cike da karfinta kuma ta gyara komai na cikin gida domin zabukanta na gaba, The Cable ta ruwaito.

Buhari ya sanar da hakan a ranar Juma'a a wani taron da yayi da kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar APC wanda ke samun shugabancin Mai Mala Buni, gwamnan jihar Yobe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng