Yanzu-Yanzu: Gwamnan Zamfara, Matawalle, Ya Sauya Sheƙa Zuwa Jam'iyyar APC

Yanzu-Yanzu: Gwamnan Zamfara, Matawalle, Ya Sauya Sheƙa Zuwa Jam'iyyar APC

  • Fadar shugaban ƙasa ta tabbatar da sauya sheƙar gwamnan Zamfara, Bello Matawalle, daga PDP zuwa APC
  • Mai taimakawa shugaban ƙasa ta ɓangaren yaɗa labarai, Bashir Ahmad, shine ya bayyana haka a wani rubutu da ya fitar
  • Sai dai a halin yanzu, gwamnatin Zamfara ba tace komai dangane da sauya shekar gwamnan ba

Fadar shugaban ƙasa ta tabbatar da sauya sheƙar gwamnan Zamfara, Bello Matawalle, daga jam'iyyar PDP zuwa Jam'iyya mai mulki ta APC.

KARANTA ANAN: PDP Ta Dare Gida Biyu, Ta Tsayar da Yan Takara 2 a Zaɓen Dake Tafe

Wannan na ƙunshe ne a wani rubutu da mai taikawa shugaban ƙasa Buhari ta ɓangaren yaɗa labarai, Bashir Ahmad, yayi a shafinsa na dandalin sada zumunta wato Facebook.

Bashir Ahmad, ya rubuta a shafinsa cewa: "Zamfara ta dawo gida, lale marhabun gwamna Matawalle."

Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle
Yanzu-Yanzu: Gwamnan Zamfara, Matawalle, Ya Sauya Sheƙa Zuwa Jam'iyyar APC Hoto: dailynigerian.com
Asali: UGC

Sai dai a halin yanzu, gwamnan Zamfara, Bello Matawalle, bai tabbatar da ficewarsa daga PDP zuwa APC ba.

A watan Afrilun da ya gabata ne gwamnonin PDP shida suka ziyarci gwamnan domin jawo hankalinsa kar ya koma APC.

KARANTA ANAN: An Kuma, Yan Bindiga Sun Sake Yin Awon Gaba da Wani Basarake, Sun Saki Matarsa

Gwamnonin sun haɗa da, gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo, Nyesom Wike na jihar Rivers, Bala Muhammed na jihar Bauchi, Darius Ishaku na jihar Taraba, Umar Fintiri na jihar Adamawa da kuma Aminu Tambuwal na jihar Sokoto.

Legit.ng hausa ta tattaro muku wasu daga cikin ra'ayoyin jama'a dangane da wannan labarin.

Comr Mustapha U Saleh, yace:

"Allah yasa silar zaman lafiyar Zamfara kenan watakila dama dan ba ɗan jamiyyar APC bane shiyasa kuka ƙi bawa Zamfaran tsaro."

Ibrahim Tajuddeen, yace:

"Yayi babban kuskure,amma ba zai gane haka a yanzun ba sai zaɓen 2023."

Anas Umar Nata'ala, yace:

"Allah dai shike bada mulki ba jam'iyya ba munyi Imani da haka saboda haka babu wani abu da zai bamu tsoro, muna bayan PDP."

A wani labarin kuma Saboda Matsalar Amfani da 55019, JAMB Ta Bayyana Sabuwar Hanyar Duba Sakamakon UTME 2021

Hukumar JAMB ta bayyana cewa ɗalibai su yi amfani da shafinta na yanar gizo domin duba sakamakon jarabawarsu

Hukumar tace a halin yanzun akwai ƙalubale da dama ta amfani da tura saƙo zuwa 55019, saboda haka an dakatar da shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262