Saboda Matsalar Amfani da 55019, JAMB Ta Bayyana Sabuwar Hanyar Duba Sakamakon UTME 2021

Saboda Matsalar Amfani da 55019, JAMB Ta Bayyana Sabuwar Hanyar Duba Sakamakon UTME 2021

  • Hukumar JAMB ta bayyana cewa ɗalibai su yi amfani da shafinta na yanar gizo domin duba sakamakon jarabawarsu
  • Hukumar tace a halin yanzun akwai ƙalubale da dama ta amfani da tura saƙo zuwa 55019, saboda haka an dakatar da shi
  • A jiya Jumu'a ne hukumar ta bayyana sakin sakamakon jarabawar UTME 2021

Hukumar JAMB ta umarci ɗaliban da suka rubuta jarabawar share fagen shiga manyan makarantun gaba da sakandire UTME su ziyarci shafin yanar gizo domin duba jarabawarsu, maimakon amfani da lambar 55019, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

KARANTA ANAN: Rundunar Yan Sanda Ta Damƙe Ɗaliban Kwalejin Fasaha 10 da Zargin Garkuwa da Abokin Karatunsu

Kakakin hukumar JAMB, Dr. Fabian Benjamin, shine ya bayyana haka a wani jawabi da aka baiwa manema labarai ranar Asabar a Abuja.

JAMB ta sanar da hanyar duba sakamakon UTME 2021
Saboda Matsalar Amfani da 55019, JAMB Ta Bayyana Sabuwar Hanyar Duba Sakamakon UTME 2021 Hoto: pmnewsnigeria.com
Asali: UGC

Dr. Benjamin, yace: "Ɗaliban da suka rubuta jarabawar zasu iya duba jarabawarsu a ko ina suke matuƙar akwai sabis din da zai basu damar shiga yanar gizo, amma a halin yanzun an dakatar da amfani da 55019."

"Mun gano cewa amfani da hanyar tura saƙo zuwa 55019 yana fuskantar ƙalubale, saboda haka muna umartar ɗalibai su garzaya shafin mu na yanar gizo domin duba sakamakonsu."

KARANTA ANAN: Gwarazan Yan Sanda Sun Yi Artabu da Yan Boko Haram, Sun Kuɓutar da Matafiya da Dama

Yadda zaka duba sakamakon JAMB a shafin yanar Gizo

Benjamin ya ƙara da cewa kowane ɗalibi zai iya ziyartar shafin hukumar na yanar gizo a www.jamb.gov.ng domin ya duba sakamakon jarabawar UTME 2021.

Daga nan sai ka shiga Efacility, zakaga wurin da aka rubuta 'Sakamakon UTME 2021'

Bayan ya buɗe, zai nuna maka wani wuri da zaka saka lambar wayar daka yi rijistar jarabawar ta bana da ita.

A wani labarin kuma Matsalar Tsaro, Yan Bindiga Sun Hallaka Matar Wani Tsohon Kwamishina

Yan bindiga sun kashe matar tsohon kwamishinan ƙananan hukumomin jihar Oyo, Mrs. Olayemi Odetomi, kamar yadda punch ta ruwaito.

Mijin matar, tsohon shugaban ƙaramar hukumar Ogbomoso ne, kuma tsohon kwamishina a jihar Oyo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel