An Kuma, Yan Bindiga Sun Sake Yin Awon Gaba da Wani Basarake, Sun Saki Matarsa
- Wasu mutane ɗauke da makamai da ake zargin masu garkuwa ne sun yi awon gaba da wani basarake a jihar Ekiti
- Oba Benjamin Oso na Eda Ile, ya fita gonarsa shi da matarsa yayin da yan bindigan suka kai masa hari
- Kwamandan Amotekun na jihar ya bayyana cewa jami'an tsaro sun afka cikin daji domin kuɓutar da shi
Wasu yan bindiga da ake zargin masu garkuwa ne sun yi awon gaba da wani basarake a jihar Ekiti, Oba Benjamin Oso, shugaban Eda Ile, a yankin ƙaramar hukumar Ekiti ta gabas, kamar yadda vanguard ta ruwaito.
KARANTA ANAN: Saboda Matsalar Amfani da 55019, JAMB Ta Bayyana Sabuwar Hanyar Duba Sakamakon UTME 2021
Wata majiya ta shaida wa manema labarai ranar Asabar a Ado-Ekiti cewa yan bindigan sun sace basaraken ne a gonarsa kuma a gaban matarsa.
Punch ta ruwaito cewa wannan shine karo na uku da yan bindiga suka kai wa sarakuna hari a cikin watanni uku.
Majiyar tace: "Oba da matarsa sun fita zuwa gona, amma sai yan bindiga suka farmake su, zasu iya sace mutum biyun duka amma sai Oba ya nemi su kyale matarsa kuma suka amince da haka."
Jami'an tsaro sun shiga daji domin kuɓutar da basaraken
Kwamandan jami'an tsaron Amotekun na jihar Ekiti, Joe Komolafe, ya tabbatar da faruwar lamarin, yace:
"Duka jami'an tsaro a jihar Ekiti da suka haɗa da sojoji, yan sanda, jami'an Amotekun, mafarauta da tawagar yan bijilanti sun shiga daji domin neman inda ɓarayin suka ɓoye basaraken."
KARANTA ANAN: Rundunar Yan Sanda Ta Damƙe Ɗaliban Kwalejin Fasaha 10 da Zargin Garkuwa da Abokin Karatunsu
Hakazalika, kakakin hukumar yan sandan jihar, ASP Sunday Abutu, yace hukumar yan sanda na ƙara nazari akan rahoton kuma bada jimawa ba zata ɗauki mataki kan lamarin.
A wani labarin kuma Gwarazan Yan Sanda Sun Yi Artabu da Yan Boko Haram, Sun Kuɓutar da Matafiya da Dama
Jami'an tsaro sun samu nasarar fatattakar yan Boko Haram a kan hanyar Maiduguri zuwa Kano.
Jami'an RRS tare da taimakon yan sanda sun fafata da yan ta'addan yayin da suka kuɓutar da matafiya da dama.
Asali: Legit.ng