PDP Ta Dare Gida Biyu, Ta Tsayar da Yan Takara 2 a Zaɓen Dake Tafe
- Rikicin cikin gida a jam'iyyar PDP ya ƙara tsananta yayin da aka gudanar da zaɓen fidda ɗan takara biyu a jihar Anambra
- Jam'iyyar ta dare gida biyu inda kowane ɓangare ya gudanar da zaɓen fidda ɗan takarar gwamnan Anambra a wuri daban
- A halin yanzun jam'iyyar PDP na da yan takara biyu a zaben gwamnan Anambra dake tafe
Rikici a jam'iyyar PDP reshen jihar Anambra ya ƙara tsananta yayin da aka bayyana yan takarar gwamna biyu daga ɓangarorin jam'iyyar biyu, bayan gudanar da zaɓen fidda ɗan takara a wurare mabambanta, kamar yadda dailytrust ta ruwaito.
KARANTA ANAN: An Kuma, Yan Bindiga Sun Sake Yin Awon Gaba da Wani Basarake, Sun Saki Matarsa
Ugochukwu Uba da Valentine Ozigbo sune yan takarar da aka bayyana daga ɓangarorin jam'iyyar PDP biyu a jihar, kamar yadda thisdaylive ta ruwaito.
Ɗaya daga cikin ɓangaren jam'iyyar bisa jagorancin Chukwudi Umeaba, sun gudanar da zaɓen fidda ɗan takara a makarantar firamare da sakandire dake Awka, inda aka bayyana Uba, ɗan uwan Chris Uba, a matsayin ɗan takara.
Sakamakon zaɓen yace: "Uba ya samu ƙuri'u 275 inda ya lallasa abokin takararsa Godwin Ezeemo, wanda ya samu ƙuri'u 114."
KARANTA ANAN: Matsalar Amfani da 55019, JAMB Ta Bayyana Sabuwar Hanyar Duba Sakamakon UTME 2021
Ɓangare na biyu ya tsayar da Valentine Ozigbo
Yayin da ɗayan ɓangaren ya gudanar da zaɓe a cibiyar taron mata dake Awka, inda aka bayyana Ozigbo, a matsayin ɗan takarar gwamna ƙarkashin PDP.
A duk cikin yan takarar, Ezeemo ne kaɗai ya halarci zaɓen fidda gwani a ɓangaren da ya tsayar da Uba, amma sauran duk sun halarci cibiyar taron mata dake Awka.
Sakamakon zaɓen ya nuna cewa: "Ozigbo ya samu ƙuri'u 62 daga cikin 200 da aka kaɗa, inda ya lallasa sauran abokan takararsa 10 a zaɓen."
A wani labarin kuma Rundunar Yan Sanda Ta Damƙe Ɗaliban Kwalejin Fasaha 10 da Zargin Garkuwa da Abokin Karatunsu
Jami'an yan sanda sun samu nasarar cafke wata tawagar masu garkuwa da mutane a jihar Ekiti.
Ɓarayin sun sace wani ɗalibi dake karatu a kwalejin fasaha ta Crown dake Ado Ekiti, inda suka karɓi kuɗin fansa miliyan N2m.
Asali: Legit.ng