Barnar Boko Haram da Na 'Yan Bindiga Basu Kai Illar Shan Miyagun Kwayoyi Ba

Barnar Boko Haram da Na 'Yan Bindiga Basu Kai Illar Shan Miyagun Kwayoyi Ba

  • Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana illolin da ke tattare da shan miyagun kwayoyi a Najeriya
  • Ya ce illar shan kwayoyi ta zarce abubuwan da ake fuskanta na ayyukan ta'addanci da na 'yan bindiga
  • Ya kuma umarni hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi da ta dauki matakin gaggawa kan lamarin

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa fataucin miyagun kwayoyi ya haifar da manyan hadurra ga Najeriya fiye da ayyukan 'yan ta'adda mabambanta.

Shugaban na Najeriya ya yi wannan bayani ne a ranar 26 ga Yuni, a yayin kaddamar da shirin yaki da miyagun kwayoyi na WADA, The Nation ta ruwaito.

Buhari, wanda ya samu wakilcin sakataren gwamnatin tarayya (SGF), Boss Mustapha, ya ce yaki da shan miyagun kwayoyi yaki ne da dole ne a yi shi ba kakkautawa.

KU KARANTA: Shinkafa Ta Wadata a Najeriya, Saura a Fara Fitarwa Kasashen Waje, in Ji RIFAN

Barnar Boko Haram da Na 'Yan Bindiga Basu Kai Illar Shan Miyagun Kwayoyi Ba
Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: Facebook

A kalamansa, cewa ya yi:

"Wannan yakin yafi barkewar tashin hankali da muke da shi a yankin Arewa maso gabashin kasar nan ko ayyukan 'yan bindiga a yankin Arewa maso yamma ko kuma ayyukan satar mutane da ya wuce misali a dukkan bangarorin kasar nan saboda yaki ne da abinda ke lalata karni uku domin na ga inda kakanni ke shan kwayoyi, iyaye na shan kwayoyi, kuma kari a nan gaba, yaransu na shan kwayoyi."

Buhari ya bukaci NDLEA ta gano boyayyum gonakin tabar wiwi

A cewar jaridar The Cable, shugaban ya bukaci hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) da ta zakulo dazuzzuka a yankuna daban-daban na kasar don gano inda ake shuka tabar wiwi.

Ya umurci hukumar da ke yaki da shan miyagun kwayoyi da ta kassara gwiwar amfani da miyagun kwayoyi tare da hukunta masu sha da masu fataucinsu a kasar.

KU KARANTA: Muna Godiya: Ganduje Ya Jinjina Wa Sojoji Bisa Kare Dajin Falgore da Jihar Kano

NDLEA ta yi nasarar cafke dillalan miyagun ƙwayoyi 231 a jihar Oyo

A wani labarin, Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi, NDLEA, reshen jihar Oyo, ta ce ta kama mutane 231 da ake zargi da safarar miyagun kwayoyi daga watan Yunin 2020 zuwa Yunin 2021, Pulse NG ta ruwaito.

Da ya ke yi wa yan jarida jawabin, a ranar Alhamis game da ayyukan da hukumar ta yi cikin lokacin da ake nazari, Josephin Obi, kwamandan jihar ya ce mutum 215 cikin wadanda ake zargin maza ne yayin da 16 kuma mata.

Mrs Obi, wacce ta samu wakilcin mataimakin kwamanda Anthony Gotar ta kuma ce rundunar ta yi nasarar kwace ganyen wiwi mai nauyin 6,355.74 da wasu kayan maye a cikin watanni shida.

Asali: Legit.ng

Online view pixel