Shinkafa Ta Wadata a Najeriya, Saura a Fara Fitarwa Kasashen Waje, in Ji RIFAN

Shinkafa Ta Wadata a Najeriya, Saura a Fara Fitarwa Kasashen Waje, in Ji RIFAN

  • Kungiyar manoma shinkafa ta yi alfaharin cewa, Najeriya ta wadata da shinkafa a wannan lokacin
  • Ta ce, a da Najeriya na samar da tan miliyan 5, amma a yanzu ana samar da sama da tan miliyan tara
  • Sai dai, har yanzu talakawan Najeriya na kokawa kan yadda abinci ya yi tsada kasar musamman shinkafa

Kungiyar Manoman Shinkafa ta Najeriya (RIFAN), ta ce noman shinkafa a kasar ya karu daga tan miliyan biyu a 2015 zuwa tan miliyan tara a 2021, Daily Nigerian ta ruwaito.

Da yake bayyana hakan a Kaduna a ranar Alhamis, Shugaban RIFAN, Aminu Goronyo, ya ce duba da yawan kayan da ake sarrafawa a yanzu, Najeriya ta shirya zama kasar da zata ke fitar da shinkafa zuwa kasashen waje.

KU KARANTA: Bayan Mutuwar Kwamishinoni 2, An Fara Addu'o'in Neman Tsari a Jihar Ebonyi

Shinkafa Ta Wadata a Najeriya, Saura a Fara Fitarwa Kasashen Waje, in Ji RIFAN
Buhunnan shinkafa | Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

A cewarsa:

“Kafin zuwan gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari a shekarar 2015, mun saba samar da kimanin shinkafa tan miliyan biyu a shekara.
“A yau, za mu iya alfahari da tan miliyan tara a shekara; akwai bambanci sosai kuma yanzu za mu iya cewa balo-balo Najeriya ta wadatu da shinkafa.''

Tsadar abinci: Ba fa zai yiwu mu yi kasa da farashin buhun shinkafa ba inji ‘Yan kasuwa

Sai dai har yanzu talakawa a Najeriya na kokawa kan tsadar da abinci ya yi, musamman shinkafa.

A bangaren kungitar RIPAN ta masu aikin gyara shinkafa a Najeriya, ta reshen jihar Kano ta yi bayanin abin da ya sabbaba tashin farashin da ake fuskanta a yau.

Jaridar Daily Trust ta fitar da rahoto inda aka ji wani daga cikin ‘ya ‘yan wannan kungiya ya na karin-haske a kan abin da ya sa buhu ya kai N23, 000.

Alhaji Abba Dantata a madadin kungiyar RIPAN, ya zanta da ‘yan jarida tare da hukumar PCACC ta jihar Kano, bayan wani zama da su ka yi a makon nan.

KU KARANTA: Ba Ni Ku Ke Cutarwa Ba: Lai Mohammed Ya Bayyana Illolin VPN Wajen Hawa Twitter

Duk da tsawon tarihin Gurasa a Kano, 'yan Gurasa sun yi barazanar daina sana'ar

A wani labarin, Masoyan Gurasa, sanannen abinci ga mutan Kano, na iya shiga mawuyacin hali domin kuwa masu sarrafa shi suna barazanar daina samar da shi saboda hauhawar farashin garin fulawa; babban sinadari don samar da gurasa.

Gurasa shine burodin gargajiya wanda akafi sani a tsakanin mutanen Kano kuma ana siyar dashi a yankuna da yawa ciki da wajen babban birni.

Hakanan mutane a wasu jihohin arewacin suma suna gudanar da kasuwancinsa duk da cewa ba za su iya daidaita dandano da kimarsa da na jama'ar Kano ba kasancewarsa abinci mai daraja da dinbin tarihi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel