Muna Godiya: Ganduje Ya Jinjina Wa Sojoji Bisa Kare Dajin Falgore da Jihar Kano

Muna Godiya: Ganduje Ya Jinjina Wa Sojoji Bisa Kare Dajin Falgore da Jihar Kano

  • Gwamnan jihar Kano ya yaba wa sojojin Najeriya bisa namijin aiki da suke tafkawa a Kano
  • Ya ce yana jinjina musu bisa kare dajin Falgore da sauran wurare a fadin jihar ta Kano
  • Ya kuma godewa al'ummar jihar Kano bisa nuna goyon bayan wajen tabbatar da tsaro a jihar

Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya yaba da kokarin da sojojin Najeriya na Brigade 3 suka yi na tsare dajin Falgore da wasu sanannun gandun daji a jihar, Daily Nigerian ta ruwaito.

Mataimakin Daraktan hulda da jama’a na rundunar sojojin 1 Division Nigerian Army na Kaduna, Ezindu Idimah ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a a Kaduna.

Mista Idimah ya bayyana cewa tsare gandun dajin da sojoji suka yi ya hana masu aikata laifuka 'yancin aiwatar da munanan ayyukansu a ciki da kewayen wadannan dazukan.

KU KARANTA: Shinkafa Ta Wadata a Najeriya, Saura a Fara Fitarwa Kasashen Waje, in Ji RIFAN

Ganduje ya yabawa sojoji saboda kare dajin Falgore da sauran wurare a Kano
Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje | Hoto: bbc.com
Asali: UGC

A cewarsa, gwamna Ganduje ya yi wannan bayani ne lokacin da ya karbi bakuncin kwamandan 3 Brigade Nigerian Army, Brig-Gen. Sinyinah Nicodemus, wacce ta ziyarci Gwamnan a ranar 23 ga Yuni, a gidan Gwamnatin Kano.

Mista Idimah ya ruwaito Ganduje na danganta zaman lafiyar da aka samu a jihar ta Kano da irin hadin kan da ke akwai a tsakanin sojoji da 'yan uwansu jami'an tsaro a jihar.

Vanguard ta ruwaito gwamnan na cewa:

"Tsaro a wannan zamani yana bukatar fasaha, wannan ya sa muka dasa kameran tsaro na CCTV don sa ido mai inganci a cikin jihar Kano."

Gwamnan Ganduje ya yaba wa jama'ar jihar Kano bisa nuna hadin kai

Mista Idimah ya ce gwamnan ya yaba wa mutanen jihar Kano saboda hadin kan da suke bayarwa wajen kai rahoton abubuwan da ba su dace ba ga jami'an tsaro.

Tun da farko a jawabinsa, Kwamandar 3 Brigade Nigerian Army, Brig-Gen. Sinyinah Nicodemus, ta yi godiya ga gwamnan saboda tallafa wa rundunar.

Nicodemus ta baiwa gwamnan tabbacin sadaukar da kai na sojoji tare da hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro wajen tabbatar da cewa tsaro da lafiyar mutane ya bunkasa.

KU KARANTA: Wata Sabuwa: Sojoji sun afkawa ofishin 'yan sanda domin kubutar da masu laifi

Babban Hafsan Sojoji Ya Kai Ziyara Imo, Ya Ce a Ragargaji IPOB Ba Sassautawa

A wani labarin, Faruk Yahaya, babban hafsan sojojin Najeriya, ya nemi sojojin da aka tura jihar Imo da su rubanya kokarinsu a yaki da haramtacciyar kungiyar IPOB a yankin kudu maso gabas, The Cable ta ruwaito.

Babban hafsan sojojin wanda ya yi kiran yayin da ya ziyarci sojojin ya ce ya zo jihar ne domin a tantance yanayin tsaro yadda yake a jihar.

An kai jerin hare-hare a jihar Imo a makonnin da suka gabata, ciki har da kisan wani jigon jam'iyyar APC, Ahmed Gulak.

Asali: Legit.ng

Online view pixel